Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara tashi a jihar Taraba, mutane da yawa sun jikkata

Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara tashi a jihar Taraba, mutane da yawa sun jikkata

  • Mutane sun shiga tashin hankali a daren Jumu'an nan a wani yankin Jalingo biyo bayan tashin wani abun Fashewa
  • Rahoto ya nuna cewa lamarin ya jefa tsoro da yanayin ɗar-ɗar a zukatan mutane kasancewar kwana uku kenan da faruwar wata fashewar duk a Taraba
  • Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, DSP Abdullahi Usman, ya ce mutum tara ne suka jikkata a lamarin

Taraba - Mutanen dake zaune a Jalingo babban birnin jihar Taraba sun shiga matsanancin tashin hankali yayin da tashin wani Bam ya jijjiga birnin.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa abun fashewan ya tashi ne a yankin Nukkai axis wanda ya haɗa iyaka da ƙaramar hukumar Ardo-Kola, jihar Taraba.

Kwanaki uku da suke gabata, mutane suka shaida tashin Bam a wannan yankin na ƙaramar hukumar Ardo-Kola.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Maziyarta da maniyyata 51 sun yi hadarin mota a Madina, mutum 8 sun kwanta dama

Taswirar jahar Taraba.
Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara tashi a jihar Taraba, mutane da yawa sun jikkata Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Lamarin ya faru ne a dai-dai lokacin da garin ya shiga cikin duhu saboda rashin wutar lantarki wanda ya samo asali daga matsalar da aka samu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani rahoto daga bakin wata majiya dake kusa a wurin da lamarin ya faru ya bayyana cewa mutane da yawan daske ne suka jikkata sanadin tashin Bam ɗin.

Haka nan wasu bayanai sun nuna cewa lamarin fashewar ya auku ne a kusa da gidan shugaban gunduma inda a kwai wata ƙaramar mashaya kuma abun ya taɓa ginin wurin.

Hukumar yan sanda ta tabbatar da adadin mutanen da abun ya shafa

Da aka tuntuɓe shi, Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Abdullahi Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Jumu'a.

Bugu da ƙari, kakakin yan sandan ya ce mutum Tara ne kacal suka jikkata amma ba zai iya bayyana adadin ɓarnar da fashewar ta yi ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya fusata, ya umarci Hafsoshin tsaro su ceto mutanen da yan bindiga suka sace

A wani labarin kuma Rundunar yan sanda ta fallasa sunaye da Hotunan mutum 12 da take nema ruwa a jallo kan hannu a ta'addanci

Kakakin yan sanda, Muyiwa Adejobi, a wata sanarwa ya ce ana zargin mutanen da aikata manyan laifukan ta'addanci a Anambra.

Ya kuma yi kira ga al'umma su taimaka wa dakarun yan sanda da bayanai domin doka ta yi aiki kan waɗan da ake zargin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel