'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Harbi Mutane, Sun Sace Dabobi Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Harbi Mutane, Sun Sace Dabobi Masu Yawa

  • Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai hari a wani kauyen Zamfara mai suna Gabake a karamar hukumar Kauran Namoda
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen garin sun kwashe kimanin awa biyu suna fafatawa da yan bindigan kafin suka ci galaba suka shiga garin
  • Yan bindiga sun raunata mutane da dama yayin artabun da suka yi, kuma daga bisani sun sace shanu da tumaki da dama na mutanen kauyen

Jihar Zamfara - Yan bindiga sun sake kai hari a wani gari a Zamfara, inda suka raunata mutane da dama kuma suka sace dabobi da yawa da ba a tabbatar da adadinsu ba.

TVC ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a kauyen Gabake da ke karamar hukumar Kauran Namoda a Jihar ta Zamfara.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Harbi Mutane, Sun Sace Dabobi Masu Yawa
'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Zamfara, Sun Raunata Mutane, Sun Sace Dabobi. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Maharan sun afka kauyen da yammacin ranar Alhamis suka yi fafata da mutanen garin na fiye da awa biyu, kamar yadda TVC ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma daga bisani yan bindigan sun yi nasarar sace shanu da tumaki mallakar mutanen garin.

Wasu cikin wadanda suka jikkata sakamakon harbinsu da aka yi da bindiga suna can a asibiti a halin yanzu suna jinya, amma ba a bayyana asibitin ba.

Ba a samu ji ta bakin yan sanda ba

Rundunar yan sandan Jihar bata riga ta ce komai ba game da afkuwar lamarin domin an nemi ji ta bakin kakakin yan sandan jihar Mohammed Shehu amma ba a same shi a waya ba.

Kimanin kilomita biyar ne nisan da ke tsakanin Kauyen Gabake da garin Kauran Namoda.

'Yan Ta'adda Sun Afka Wa Mutane a Masallaci Yayin Buɗe-Baki, Sun Kashe 3 Sun Sace Wasu Da Dama

Kara karanta wannan

Mu muka kai harin Bam mashaya a jihar Taraba, Kungiyar ISWAP

A wani labarin, A ranar Talata ‘yan bindiga sun kai farmaki masallaci inda suka afka wa wa mutane yayin da suke tsaka da yin buda-baki, wanda ya ja suka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta gano yadda ‘yan ta’addan suka isa da yawansu, har suka sace wasu da yawa a masallacin sannan suka zarce da su inda ba a sani ba.

An tattaro bayanai akan yadda lamarin ya auku a kauyen Baba Juli da ke karamar hukumar Bali a cikin Jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel