Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sun Sace Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga a Anambra

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sun Sace Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga a Anambra

  • Shugaban Kungiyar Makiyayan Shanun Najeriya ta Miyetti Allah (MACBAN), na Kudu maso Gabas, Alhaji Gidado Siddiki ya koka akan yadda ‘yin bindiga suka sace mambobin kungiyar guda goma
  • A cewarsa, sun hada da kwace shanu dari uku yayin da suka kai farmaki rukunin gidajen Fulani da ke Obene a karamar hukumar Ogbaru cikin Jihar Anambra ranar Asabar
  • A cewarsa yanzu haka masu garkuwa da mutanen su na bukatar Naira miliyan hudu da bindiga daya a matsayin kudin fansa duk da wadanda suka sace masu kananun karfi ne

Anambra - Alhaji Gidado Siddiki, shugaban Kungiyar Makiyayan Shanun Najeriya ta Miyetti Allah (MACBAN) na reshen Kudu maso Gabas, ya koka akan yadda ‘yan bindiga suka sace ‘yan kungiyarsu 10 da shanu 300 a yankin, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Jirgin sojin sama ya ragargaji maboyar 'yan bindiga a Taraba

Miyetti Allah: Ƴan Bindiga Sun Sace Mambobinmu 10 Da Shanu 300, Sun Buƙaci N4m Da Bindiga a Anambra
'Yan bindiga sun yi garkuwa da mambobinmu 10 da shanu 300, su na bukatar N4m da bindiga daya a Anambra, Miyetti Allah. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Siddiki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai suka yi da shi a Awka inda ya ce lamarin ya auku ne a rukunin gidajen Fulani da ke Obene a karkashin karamar hukumar Ogbaru cikin Jihar Anambra, ranar Asabar 23 ga watan Afirilun 2022 da misalin karfe 1:30 na dare.

Ya ce ‘yan bindigan da za su kai 40 sun kai wa makiyayan farmaki a gidajensu ne lokacin da su ke bacci inda su ka kwace dabbobinsu da karfi da yaji.

Sun bukaci N4m da bindiga daya a matsayin kudin fansa

A cewarsa kamar yadda Nigerian Trubune ta nuna, sun isa yankin ne da miyagun makamai ciki har da bindigogi, adduna, layu da sanduna.

Ya ci gaba da cewa har sun fara magana da ‘yan uwan wadanda su ka sace inda su ka bukaci Naira miliyan hudu da bindiga a matsayin kudin fansa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Kamar yadda ya shaida:

“Yanzu haka batun da mu ke yi, na kai rahoto ofishin ‘yan sanda da DSS don a fara daukar mataki.”

Ya bukaci masu garkuwa da mutanen su saki mambobin, kasancewar duk masu kananun karfi ne.

Ya koka akan yadda ake daura laifin duk wani farmaki ga Fulani

Ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda ake mayar da harkar makiyaya siyasa wanda hakan ya ke haifar da tashin hankali a kasa, inda ya ce ana alakanta duk wani laifi ne da makiyaya a ko wanne lokaci.

Siddiki ya yaba wa Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo akan kokarin kawo zaman lafiya da sasanci a jihar da kuma yankin Kudu maso Gabas.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Malamin Addini: Mutane 2 ne kadai masu kyakkyawar manufa cikin masu son gaje Buhari

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel