Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6

Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6

Borno - Dakarun jami'an hadin guiwa na MNJTF sun halaka mayakan ta'addancin Boko Haram 27 da na ISWAP dake yankin tafkin Chadi a Najeriya, jamhuriyar Nijar da Kamaru, Channels TV ta ruwaito.

A cigaba da ayyukan tsabtace tafkin da dakarun ke yi, sun ceto wasu mata shida da 'yan ta'addan suka yi garkuwa dasu daga jihohin Adamawa, Borno, Gombe da Yobe daga watan Oktoban 2020 zuwa Afirilun 2021.

Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6
Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Kamar yadda mai magana da yawun MNJTF, Kanal Muhammad Dole ya sanar, an halaka kusan 'yan ta'adda 20 ne a ragargazar da dakarun sojin sama suka yi bayan a sirrance sun gano cewa 'yan ta'addan na boyewa a Tumbun Fulani da Tumbun Rago.

Har ila yau, yayin da jami'an MNJTF din na sintiri a yankin Ngagam - Kabalewa da N'guigmi, sun yi arangama da wasu 'yan ta'adda da ke tserewa inda suka halaka biyar daga ciki, suka lalata motar yaki biyu tare da kwace makamai da harsasai masu yawa.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cike da tashin hankali, soja daya ya rasa ransa yayin da wasu kadan suka jigata. A halin yanzu suna samun kulawar masana kiwon lafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata arangama, dakarun sashi na daya a Kamaru sun halaka 'yan Boko Haram biyu a yankin Toumbum, Kerenua da Chikingudu.

A karshen arangamar farkon da aka yi wuraren Tumbun Fulani da Tumbun Rago, an samo firgitattun mata shida wadanda sojojin suka taimaka musu tare da fito dasu.

Daga bisani an kwashe matan inda aka tafi dasu Maiduguri a binciki lafiyarsu kafin a mika su ga hukumomin har su kai ga iyalansu.

Binciken farko ya nuna cewa wadanda suka tsiran 'yan asalin Borno, Gombe da Yobe ne wadanda aka sace a lokuta daban-daban.

Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

A wani labari na daban, 'yan ta'adda sun gamu da gamonsu a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno yayin da dakarun sojin Najeriya suka ceto mata 43, kananan yara da wani tsoho.

Dakarun sojin Najeriya na bataliya ta 202 sun lallasa 'yan ta'addan Boko Haram yayin da suka je kakkabar daji a yankin arewa gabas na jihar Borno, PR Nigeria ta ruwaito.

Birged ta 21 dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno ta na karkashin kulawar Birgediya Janar Waidi Shayibu, wanda shi ne babban hafsan soja mai bai wa Div 7 umarni na rundunar sojin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel