Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun bindige fitaccen kwamandan IPOB

Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun bindige fitaccen kwamandan IPOB

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar bindige wani dan ta'adda a Banana Junction dake karamar hukumar Orlu ta jihar Imo
  • An gano cewa dan ta'addan shi ne kwamandan IPOB na yankin kuma sun fito tabbatar da dokar zaman gida dole ne
  • Sojojin sun sanar da yadda 'yan ta'addan suka bude musu wuta amma suka nuna musu gwarzantakarsu wanda yasa sauran suka tsere

Imo - Dakarun sojin Najeriya sun bindige wani dan bindiga wanda aka gano cewa kwamandan 'yan awaren IPOB ne a Imo.

Dakarun sun ce sun yi arangama da 'yan awaren wadanda suka fara harbinsu a Banana Junction dake karamar hukumar Orlu ta jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun bindige fitaccen kwamandan IPOB
Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun bindige fitaccen kwamandan IPOB. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jaridar Solacebase ta rahoto cewa, sun ce suna tabbatar da dokar zaman gida dole ce kan jama'ar jihar.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga, sun tura da yawa lahira a jihar Arewa

Mai magana da yawun sojojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya yi bayani a Abuja a ranar Litinin yace an halaka dan bindigan ne yayin musayar wuta da suka yi a yankin Ihioma dake Orlu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nwachukwu ya ce bayan ganin dakarun, 'yan ta'addan IPOB/ESN sun tsere a wata mota kirar Toyota Highlander kalar bula.

"A musayar wuta da aka yi, an halaka daya daga cikinn 'yan ta'addan yayin da sauran suka tsere. Sojoji a halin yanzu suna binciken yankin domin damko sauran miyagun da suka tsere."
"Sakamakon ruwan wutan da suka fuskanta tare da hana su 'yancin da sojoji suka yi, kungiyar ta koma yada karairayi da farfaganda ga jama'a.
"Sun dinga yada wani bidiyo da suka gurbata a kafafen yada zumuntar zamani inda suke zargin sojojin da cutar dasu. A yi watsi da wannan farfagandar baki dayanta," takardar tace.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Jami'an tsaro sun sheke Ikonso, kwamandan IPOB, mashiryin hare-hare a kudu

A wani labari na daban, jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya da takwarorinsu na rundunar soji da farin kaya, a wani aikin hadin guiwa da suka yi a sa'o'in farko na ranar Asabar, sun tsinkayi hedkwatar 'yan ta'addan IPOB dake kauyen Awomama dake karamar hukumar Oru ta gabas a jihar Imo inda suka halaka 'yan tada kayar baya.

'Yan ta'addan ne suke da alhakin kai hari hedkwatar 'yan sandan jihar da gidan gyaran hali a ranar 5 ga watan Afirilun 2021. Sun kai wasu jerin farmaki ga jami'an tsaro da wurare da suke a yankunan kudu maso gabas da kudu kudu na kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel