Mutum 13 da suka ba Buhari shawara a yafewa tsofaffin Gwamnonin da ke gidan yari

Mutum 13 da suka ba Buhari shawara a yafewa tsofaffin Gwamnonin da ke gidan yari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga wasu mutanen da kotu ta samu da aikata laifi
  • Tsofaffin gwamnonin Taraba da Filato, Jolly Nyame da Joshua Dariye sun shiga wannan jirgin ceto
  • Kwamitin PACPM da aka kafa a shekarar 2018 ne ya ba gwamnatin Buhari shawarar a yi masu afuwa

Abuja - Jaridar Premium Times ta kawo rahoto da ya nuna diddikin yadda shugaban Najeriya ya yafewa wasu mutane 159 da aka samu da laifi.

Kwamitin Presidential Advisory Committee on Prerogative of Mercy na PACPM da Ministan shari’a ne ya kawowa gwamnati wannan shawara.

Shugaban kasa yana da iko a karkashin sashe na 175 na dokar Najeriya da ya yi wa duk wanda yake so afuwa, kuma komai irin girman laifin na sa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Mai girma Muhammadu Buhari ya karbi shawarar kwamitin Abubakar Malami, ya yafewa masu laifin bayan kai maganar gaban majalisar kolin kasa.

Majalisar koli da ke dauke da tsofaffin shugabannin Najeriya da tsofaffin Alkalan Alkalai na kasa sun amince da wannan afuwa kamar yadda aka bukata.

Jaridar ta tattaro sunayen duka mutanen da suke cikin wannan kwamiti na shugan kasa:

Shugaban kasa
Shugaba Buhari a wani taro Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Su wanene 'yan kwamitin

1. Abubakar Malami (Shugaban kwamiti) – AGF

2. Jim-Jaja Ibiwari (Sakataren kwamiti) – Darekta a ma’aikatar ayyuka na musamman

3. Anthonia A. Ekpa – Sakataren din-din-din a ma’aikatar ayyuka na musamman

4. Leticia Ayoola-Daniels – Wakilin ma’aikatar shari’a

5. Raphael Ibinuhi – Wakilin hukumar gidajen gyaran hali

6. CP Shehu Gwarzo – Wakilan rundunar ‘yan sanda

7. Albert Uko – Wakilin kungiyar CAN

8. Auwalu Yadudu – Wakilin kungiyar Jamaatul Nasri Islam (JNI)

Kara karanta wannan

Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari

9. Yetunde Haastrup – Wakilin hukumar NHRC

10. Lady Obodoukwu – ‘Yar kishin kasa kasa

11. Lucy Ajayi – ‘Yar kishin kasa

12. Joshua Mbu – ‘Dan kishin kasa

13. B.A. Ogunbambi – ‘Dan kishin kasa

Yadda aka bi - Malami

Ministan shari’a na kasa wanda shi ne babban lauyan gwamnatin tarayya ya ce kwamitin sun tattauna da jama’a tare da nazari kafin su cin ma matsaya.

Abubakar Malami SAN ya ce sun karbi bayanai daga gidajen gyaran halin da ke Najeriya kafin su bada shawarar a yafewa wadannan mutane da suke daure.

A kan wani dalili?

An ji Garba Shehu ya na cewa majalisar koli tayi tunani kafin ta dauki matakin yin afuwar. A cewarsa, ba haka nan shugaban kasa ya yi abin da kai ba.

Hadimin ya ce an duba uzurin rashin lafiya da tsufar Jolly Nyame da Joshua Dariye, sannan kuma an yi wasu mutanen dabam da ba su shara ba afuwa.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

Asali: Legit.ng

Online view pixel