Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

  • Gwamnan jihar Benue ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa yafewa gwamnonin Najeriya biyu
  • Gwamnonin sun kasance a gidan yari na wani lokaci bisa hukuncin kotu kan badakalar kudi lokacin da suke gwamnoni
  • Shugaba Buhari ya yafe musu tare da wasu fursunoni da dama a taron majalisar kolin shugabannin Najeriya

Benue - Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, a ranar Juma’a, ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisar kolin kasa bisa afuwar da suka yi wa tsaffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Sanata Joshua Dariye da Rabaran Jolly Nyame.

Dariye da Nyame dai na zaman gidan kaso ne a gidan yari a Kuje da ke Abuja, biyo bayan hukuncin da kotuna ta yanke musu kan badakalar kudi a lokacin da suke gwamnoni tsakanin 1999 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bugi Ƙirji, Ya Ce Yana Ta Cika Wa 'Yan Najeriya Alƙawuran Da Ya Ɗauka Yayin Kamfen Ɗin Zaɓen 2015

Martanin Ortom kan yafewa gwamnonin Najeriya biyu
Mun gode Buhari: Gwamnan PDP ya ji dadin yafewa tsaffin gwamnoni 'yan rashawa | Hoto: channelstv.com
Asali: Facebook

A yayin da Ortom ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na ARISE makwanni biyu da suka gabata, ya roki gwamnatin tarayya da ta sake duba shari’ar Dariye da Nyame, da nufin yi musu afuwa, inji rahoton Daily Trust.

A ranar Alhamis ne Majalisar Kolin karkashin jagorancin Buhari ta yi taro a Abuja inda rahotanni suka ce sun yi la’akari da yin afuwa ga Dariye, Nyame da sauran wadanda da ke zaman gidan kaso.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ortom, Nathaniel Ikyur ya fitar, ya ce gwamnan ya godewa shugaba Buhari da majalisa da kuma gwamnatin tarayya bisa wannan matakin duk da cewa ya yarda cewa lallai an koyi darassu masu amfani daga lamarin.

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga abokai da iyalai da abokan siyasa na shugabannin biyu da suka ba su goyon baya a tsawon lokacin da suke gidan yari, kamar yadda AIT ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bayan satar dukiyar al’umma, Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

Ya kara da cewa yanzu Dariye da Nyame za su sake ganawa da iyalansu kuma za su sake rayuwa cikin jin dadi.

Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

A wani labarin, Majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

Asali: Legit.ng

Online view pixel