Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari

Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga al'ummar kasar Afrika ta kudu bisa annobar ambaliyar da ta afka musu
  • Shugaban kasa yace ya yi matukar kaduwa kuma cike yake da bakin ciki bisa abinda ya faru
  • Ana fargabar cewa kawo yau Asabar, kimanin mutum 300 ne suka mutu a wannan annoba

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa al'ummar kasar Afrika ta kudu bisa annobar ambaliyar ruwan sama da ta auku a yankin KwaZulu-Natal.

Sakamakon ruwan saman da aka fara tun ranar Litinin, an ruwaito Ministan harkokin gargajiyan kasar, Sipho Hlomuka, da cewa kawo ranar Laraba mutum 259 sun rasa rayukansu.

Gwamnatin yankin KwaZulu-Natal tace wannan ambaliyar ce mafi muni a tarihin kasar.

Kawo ranar Juma'a, sama da mutum 300 ne suka mutu, riwayar CNN.

Kara karanta wannan

Nayi matukar farin cikin yafewa Dariye da Nyame, Buhari ya amsa kira na: Jonah Jang

Shugaba Buhari
Nayi matukar kaduwa bisa ambaliyar ruwan sama a kasar Afrika ta Kudu, Shugaba Buhari Hoto: Presidency

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A sakon da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya saki ranar Juma'a, ya ce Shugaba Buhari ya yi matukar kaduwa kuma ransa ya baci sosai, TheCable ta ruwaito.

Yace:

"Na yi matukar kaduwa bisa annobar da jefa makwabtanmu cikin mugun hali da rashin rayuka."

Buhari ya yi kira ga sauran shugabannin Afrika su hada kai wajen samar da hanyoyin dakile illolin sauyin yanayi.

Gwamnatin Buhari ta fara rabon ton 40,000 na hatsi don Easter da Azumi ga talakawa

Ministan aikin noma da raya karkara, Dr. Mohammad Mahmood Abubakar, ya kaddamar da shirin rabon ton 40,000 na kayan hatsi ga talakawa a fadin Najeriya.

Ya bayyana cewa wannan kayan hatsi da aka saki zai rage hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa kuma ya tabbatar da cewa zai kawar da talauci.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

A taron kaddamar da rabon kayan hatsin da sansanin yan gudun hijra dake Karmajiji, birnin tarayya Abuja, Ministan yace an fara rabon ne bisa umurnin Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel