Shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaro, ministoci kan batun tsaron Najeriya

Shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaro, ministoci kan batun tsaron Najeriya

  • Bayan kammala hidimar jam'iyyar APC a jiya Laraba, a yau Alhamis ne shugaba Buhari ya gana da manyan jami'an gwamnati
  • Shugaban ya tattaunawa batutuwan tsaro tare da hafsoshin tsaro, ministoci da masu ruwa da tsaki a gwmanatin Najeriya
  • An fara ganawar ne da misalin karfe 10 na safe a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja

FCT, Abuja - Labarin da Legit.ng Hausa ke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar wata ganawa da wasu ministoci da shugabannin hukumomin tsaro a fadarsa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 10 na safe, ya biyo bayan shawarwarin da majalisar dokokin kasar ta bayar ne kan duba lamarin rashin tsaro a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Matsalolin Najeriya: Buhari Ba Shi Da Laifi, Gwamnoni Ne, In Ji Mallam Isa Yuguda

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd.) sun halarci taron.

Ganawar Buhari da hafsoshin tsaro
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaro kan batutuwan tsaron Najeriya | Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Ministocin tsaro Bashir Magashi; Cikin gida, Rauf Aregbesola; da kuma harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama su ma suna wurin taron.

Shugaban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Isiaka Oladayo Amao duk sun hallara.

Babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor ne bai samu halarta, amma ya tura wakili, inji rahoton The Nation.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba Usman; Babban Darakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa'i Abubakar.

Kara karanta wannan

Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

A wani labarin, a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu 2022, Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya koka a game da yadda sha’anin tsaro ya kara tabarbarewa a Najeriya.

Gidan talabijin na Channels TV ya rahoto Douye Diri yana cewa an fi samun kwanaciyar hankali a shekarar 2015, kafin APC ta karbi mulkin kasar nan.

Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke garin Yenagoa, Douye Diri ya shaidawa wasu manyan jami’an tsaro cewa batun tsaro ya cabe a yankin Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel