Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa

Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa

  • Wani Alfa ya shiga jerin masu neman hawan kujerar shugaban kasa inda Buhari ya sauka a 2023
  • Alfa Olasupo Akinola yace dubi ga irin halin kunci da yan Najeriya ke ciki, ana bukatar mai tsoron Allah
  • Za'a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya a watan Febrairun 2023

Ibadan - Wani matashin Malamin addini dan shekara 40 ya ayyana niyyar shiga takarar neman kujeran shugaban kasar Najeriya a zaben 2023 da zai gudana a Febrairu.

Alfan mazaunin garin Ibadan, jihar Oyo mai suna Olasupo Afeez Akinola ya ce zai yi takara ne karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Olasupo ya bayyanawa mabiyansa cewa ubangiji ne ya umurcesa ya shiga takara saboda yan Najeriya na cikin bakin talauci kuma ana bukatar shugaba mai tsoron Allah, rahoton TheNation.

Kalli hotunansa:

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 10 a Kudu da Arewacin Najeriya da sai inda karfinsu ya kare a takarar Tinubu

Matashi Alfa
Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa Hoto: TheNation
Asali: Facebook

Matashi Alfa
Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa Hoto: TheNation
Asali: Facebook

Takara a 2023: Tinubu, Osinbajo da sauran jiga-jigan APC da suka ayyana nufin gaje shugaba Buhari

Zuwa yanzun akalla mutum Bakwai suka ayyana aniyarsu ta neman takarar shugaban ƙasa a 2023 ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC.

Jerin yan takarar da suka faɗa wa Duniya nufin su a hukumance

1. Bola Ahmed Tinubu

2. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

3. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi

4. Tsohom gwamnan Abia kuma Sanata mai ci, Sanata Orji Kalu

5. Tsohon gwamnan Imo kuma Sanata mai ci, Sanata Rochas Okrocha.

6. Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi

7. Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo

Ɗaga cikin duka waɗan nan yan yakara, Bola Tinubu, na cigaba da kai ziyara sassan kusoshin jam'iyya da ya haɗa da majalisar tarayya, yana baran goyon bayan su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan ta'adda na ruwan wuta a kauyuka 2 na Shiroro a jihar Niger

Asali: Legit.ng

Online view pixel