Matsalolin Najeriya: Buhari Ba Shi Da Laifi, Gwamnoni Ne, In Ji Mallam Isa Yuguda

Matsalolin Najeriya: Buhari Ba Shi Da Laifi, Gwamnoni Ne, In Ji Mallam Isa Yuguda

  • Tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Mallam Isa Yuguda ya yi wa gwamnonin jihohi 36 da ke kasar nan wankin babban bargo a ranar Laraba
  • Yuguda ya zarge su da kasancewa masu son kai kuma marasa mayar da hankali akan ci gaban kasa, inda ya ce laifinsu ne matsalolin Najeriya ba Shugaba Buhari ba
  • Ya yi wannan furucin ne a Abuja jim kadan bayan an nada shi Darekta-Janar kuma shugaban kungiyar kamfen din shugaban kasa na Tein Jack-Rich

FCT, Abuja - A ranar Laraba, Mallam Isa Yuguda, tsohon gwamnan Jihar Bauchi ya ce duk laifin gwamnoni 36 ne matsalolin da Najeriya ta ke fuskanta, The Punch ta ruwaito.

A cewarsa, ya kamata a dena mayar da laifi akan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, saboda gwamnonin ne masu son kai sannan ba sa mayar da hankali akan ci gaba.

Kara karanta wannan

Al-mundahana: EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m

Yuguda ya fadi hakan ne a Abuja bayan kammala nadin shi Darekta-Janar kuma shugaban Kungiyar Kamfen din shugaban kasa na Tein Jack-Rich.

Matsalolin Najeriya: Buhari Ba Shi Da Laifi, Gwamnoni Ne, In Ji Mallam Isa Yuguda
A kan gwamnoni ya kamata a daura laifin matsalolin Najeriya ba Buhari ba, Yuguda. Hoto: The Punch.
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jack-Rich hamshakin dan kasuwar mai ne wanda ke neman takarar shugaban kasa daga jihar Ribas

Jack-Rich hamshakin dan kasuwar mai ne kuma shi ne mai Kamfanin Belema Oil. Asalin dan Jihar Ribas ne sannan yanzu haka yana neman tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC.

The Punch ta ruwaito yadda tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma ministan sufuri, Rotimi Amaechi ma ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Kamar yadda Yuguda ya ce:

“Na yi aiki da gwamnoni da dama a karo na farko da na biyu da na rike gwamna kuma na san irin tunaninsu. Abin ban takaici ne yadda gwamnonin Najeriya ba sa mayar da hankalin wurin ci gaba. Wani abu ne can daban ke ransu.

Kara karanta wannan

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

“Idan da sun mayar da hankali kan ci gaban Najeriya da tuni an samu sauyi mai tarin yawa. Ba laifin shugaban kasa ba ne, komin kokarinsa idan gwamnoni ba su yi nasu ba babu wani abin kirki da zai samu.”

Yayin amsar sabon mukamin na shi, Yuguda ya ce ya samu kansa akan wani aiki na musamman wanda matashi ke neman APC ta tsayar da shi dan takarar shugaban kasa.

Ya kwatanta Jack-Rich a matsayin mutum mai ilimi sannan kuma dan kasuwa mai tarin nasarori, ya ce ana sa ran zai kawo karshen matsalolin Najeriya idan an ba shi dama.

Yuguda ya ce Jack-Rich na matasa ne

A cewarsa:

“Jack-Rich na matasa ne da kuma masu matsakaicin shekaru, ba na tunanin zai yi aiki da tsofaffin da ke Najeriya saboda babu wani abin a zo- a gani da su ka yi wa kasar nan.
“Ban san wanda Ubangiji ya ba damar zaben zama kabilar Kanuri, Hausa, Igbo, Yoruba, Ijaw ko wani yare na daban ba. Daga Al-Qur’ani har Bibul su na yi mana jagora ne, sai dai abubuwa marasa kyau su na faruwa ne saboda mun manta koyarwar addinanmu.”

Kara karanta wannan

Matashi Alfa a jihar Ibadan ya shiga takarar neman kujerar shugaban kasa

Ya ci gaba da cewa:

“Ya kamata mu kawo karshen wadannan munanan abubuwan da rabe-raben kawuna kuma Jack-Rich zai yi iyakar kokarinsa. Mafita akan matsalolin da mu ke fuskanta ne Jack-Rich.”

Dama tun farko sai da Jack-Rich ya bukaci mutanen yankuna daban-daban na kasar nan da su kasance masu neman masalaha, domin hakan ne kadai zai bunkasa kasar nan.

A cewarsa, shugabanci mara kyau ne matsalar Najeriya, hakan ya sa ya yi alkawarin samar da shugabanci mai nagarta da kuma hadin kan kasar nan idan aka ba shi damar gadar kujerar Buhari a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel