Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

  • Gwamnan jihar Bayelsa ya ce sha’anin tsaro ya tabarbare a gwamnatin Muhammadu Buhari mai-ci
  • Sanata Douye Diri ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen kawo zaman lafiya a Arewa
  • Amma Buhari yana ganin ‘Yan Najeriya sun fi samun tsaro yanzu fiye da yadda ake ciki kafin zuwansa

A ranar Talata, 19 ga watan Afrilu 2022, Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya koka a game da yadda sha’anin tsaro ya kara tabarbarewa a Najeriya.

Gidan talabijin na Channels TV ya rahoto Douye Diri yana cewa an fi samun kwanaciyar hankali a shekarar 2015, kafin APC ta karbi mulkin kasar nan.

Da yake jawabi a gidan gwamnati da ke garin Yenagoa, Douye Diri ya shaidawa wasu manyan jami’an tsaro cewa batun tsaro ya cabe a yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

Mai girma gwamnan ya bayyana cewa kashe-kashen da ake yi a jihohin Arewa sun shafi yankin kudu, ya ce wadannan abubuwa su na maida kasar baya.

Abin da Gwamna Diri ya fada

“Na tabbata za ku yarda da ni cewa abubuwa sun fi muni a yanzu a kan a 2015. Wajibi ne gwamnatin tarayya ta kara kokarin da ta ke yi.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan ba haka ba, talakawa za su koya masu hankali, sun san abin da ya kamata su yi a 2023.”
Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: @Buhari Sallau
Asali: Facebook
“Idan wani sashe na kasar nan yana cikin wani mugun hali, zai shafi sauran wurare. Babu zaman lafiya a Kaduna da sauran jihohi na Arewa.”

Dole a kawo zaman lafiya

Jaridar Vanguard ta rahoto gwamnan na Bayelsa yana cewa ya zama dole gwamnatin da Muhammadu Buhari yake jagoranta ta tashi-tsaye a kan batun.

Kara karanta wannan

Mai fada a ji ga Buhari: Ka san yadda zaka yi Jonathan ya gaje ka a zaben 2023

Sanata Diri yana so a kawo karshen kashe-kashe, ta’adanci da garkuwa da mutanen da ake yi.

Shugaba Buhari ba zai yarda ba

Wannan jawabi ya ci karo da abin da Mai girma Muhammadu Buhari ya fada kwanan nan na cewa an inganta sha’anin tsaro a karkashin gwamnatin APC.

An ji shugaban Najeriyar a taron majalisar NEC na jam’iyyar APC yana cewa abubuwa sun yi kyau yanzu idan aka kamanta da zamanin Dr. Goodluck Jonathan.

Hare-haren Boko Haram

An ji labarin cewa mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province sun kai wani hari a Chibok, sun kashe ‘dan banga, sun dauke wasu 'yan mata shida.

Haka zalika mu na da labari ‘Yan ta’addan da aka fi sani da ISWAP ko Boko Haram shiga wani kauye da ake kira Kawori a garin Geidam, sun yanka mutum tara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel