Wike: Idan da Ganduje ya fito takarar shugaban kasa, da tuni na janye

Wike: Idan da Ganduje ya fito takarar shugaban kasa, da tuni na janye

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tabbatar da cewa da Ganduje ya fito domin ceto Najeriya, babu shakka shi zai janye daga takarar
  • A cewar Wike wanda ya kai wa ganduje ziyara har jihar Kano, yana da tabbacin gwamnan Kanon zai taimaka masa wurin cikar burinsa na mulkar Najeriya
  • Wike ya kara da sanar da cewa Najeriya na zuba da jini kuma hakkin kowa ne ceton ta, don haka ya ga zai iya mulkar kasar

Kano - Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce idan da Abdullahi Ganduje, takwaransa na jihar Kano ya fito takarar shugabancin kasa a 2023, da babu shakka sai ya janye.

Wike ya sanar da hakan ne a Kano yayin wata ziyara da ya kaiwa Ganduje a ranar Litinin.

Daily Post ta rahoto cewa, ya sanar da Ganduje cewa, zai yi watsi da burinsa na zama shugaban kasa idan da gwamnan Kano ya shiga tseren ceto Najeriya.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Wike: Idan da Ganduje ya fito takarar shugaban kasa, da tuni na janye
Wike: Idan da Ganduje ya fito takarar shugaban kasa, da tuni na janye. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya yi kira ga masu hannu da shuni da su yi aiki domin tabbatar da hadin kan kasar nan ba tare da duban banbancin siyasa ba, The Cable ta ruwaito.

Yace a duk lokacin da abu yayi tsanani, jajirtattun mutane ake bukata su jagoranci kasar nan inda ya kara da cewa yana da gogewar mulkar kasar.

"Ba sai na fadi ba, kasar nan ba daidai take ba kuma ya dace a dauka matakan gaggawa wurin ceto kasar wanda ni na fito ne in yi gyara," Wike yace.
"Daga duk inda ka zabi kallon Najeriya, zubar jini take yi kuma tana bukatar kokarin dukkanmu wurin ceto ta.
"Idan da Ganduje ya fito takarar shugabancin kasa, wasu daga cikinmu da gudu za su janye burinsu. Amma mun gode Allah bai fito takara ba kuma ina da tabbacin zai taimake ni in samu."

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

A bangarensa, Ganduje ya ce ya matukar jin dadin ganin tawagar yankin neman zaben Wike a matsayin shugaban kasa.

Ya ce a bayyane ya nuna yadda ya yarda da Najeriya mai cike da hadin kai.

"Banbancin siyasa kada ya mayar da mu sakarkaru; babancinmu babban al'amari ne duk da mun kasa amfani da shi yadda ya dace. Dole ne kowannenmu ya yi kokarin ganin ya sauya halin da ake ciki," yace.

Bidiyon yadda Ganduje ya kalli Wike ido cikin ido ya fada masa cewa ba zai kai labari ba a 2023

A wani labari na daban, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kalli takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike a cikin ido sannan ya sanar masa da cewa ba zai yi nasara ba a kokarinsa na son gaje shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2023.

Ganduje ya yi sakin zancen ne a lokacin da Wike ya ziyarci jiharsa a yayin da yake ci gaba da tuntubar al’umman yankin arewacin Najeriya domin samun goyon bayansu.

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne Amaechi ya kai wa shugaban APC jakunkunan kudi yayin da ya ziyarcesa?

Sai dai kuma cike da barkwanci, Gwamna Ganduje ya ce Wike na birge shi saboda kasancewarsa daga cikin mutane masu karfin gwiwa, wanda koda sun fadi a yau za su sake tashi domin sake gwada sa’arsu a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel