Yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa da suka sace a Neja idan ba a biya kudin fansa N1.7m ba

Yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa da suka sace a Neja idan ba a biya kudin fansa N1.7m ba

  • Wasu masu garkuwa da mutane da suka sace wata budurwa a jihar Neja sun tunkari iyayenta da babban bukata
  • Maharan sun yi barazanar aurar da matashiyar budurwar idan har ba a biya kudin fansarta naira miliyan 1.7 ba
  • Suna son a kawo masu zunzurutun kudi naira miliyan 1 sannan a sayo masu babur da sauran N750,000 kafin su sake ta

Neja - Yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa mai shekaru 21 da suka sace daga wani gari a jihar Neja idan har iyayenta basu biya kudin fansarta naira miliyan 1.7 ba, Vanguard ta rahoto.

A ranar Asabar da ya gabata ne dai aka yi garkuwa da wasu mutane a hanyar Tapila-Gwada a karamar hukumar Shiroro ta jihar, kuma budurwar na daya daga cikinsu.

A yayin farmakin da suka kai garin, wanda yake tafiyar minti 30 daga garin Minna, babban birnin jihar, wasu mazauna garin Tapila sun yi nasarar tserewa jim kadan bayan yan bindigar sun sace su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige sabon zababben kansilan APC a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2

Yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa da suka sace a Neja idan ba a biya kudin fansa N1.7m ba
Yan bindiga sun yi barazanar aurar da wata budurwa da suka sace a Neja idan ba a biya kudin fansa N1.7m ba Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai kuma, yan bindigar sun tafi da wasu adadi na mutane da ba a sani ba kuma har yanzu suna tsare a hannunsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa da farko yan bindigar sun nemi a biya kudin fansa naira miliyan 2, sannan suka rage zuwa naira miliyan 1.7 bayan sun zanta da iyayen yarinyar a daren ranar Talata.

Sun bukaci iyayen yarinyar mai suna Deborah su biya zanzurutun kudi naira miliyan daya sannan su siyo masu babur da sauran N750,000.

Gwaggon yarinyar wacce ta tabbatar da lamarin ta ce:

“Wadannan mutanen sun bukaci kudin fansa naira miliyan daya, sannan a siya masu babur na kimanin 750,000, ko kuma su aurar da daya daga cikinsu. Tsawon awa daya, suna kan waya sannan dan uwana na ta rokonsu, yana kuka.”

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa kakakin yan sandan jihar wanda yayi martani kan harin, Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa sun yi nasarar dakile harin sannan sun dawo da zaman lafiya garin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar Filato

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun kashe wani malamin sakandare a Zamfara

A wani labari na daban, wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun bindige wani malamin makarantar sakandare har lahira a jihar Zamfara, TVC News ta rahoto.

An bindige malamin makarantar mai suna Tukur Kurma a lokacin da yan bindigar suka bude wuta kan matafiya a hanyar Tashar Taya, yankin Danzaurfe da ke babban titin Anka-Dakitwakwas-Gummi a yammacin ranar Talata, 19 ga watan Afrilu.

Yan bindigar sun harbi motar mai tafiya a lokacin da direban ya ki tsayawa tare da wasu ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel