Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun kashe wani malamin sakandare a Zamfara

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun kashe wani malamin sakandare a Zamfara

  • Wasu yan bindiga sun farmaki yankin Danzaurfe da ke babban titin Anka-Dakitwakwas-Gummi jihar Zamfara a yammacin ranar Talata
  • Maharan sun bude wuta kan wasu jama'a da ke kan tafiya inda suka hallaka wani malamin makarantar sakandare
  • Malamin da aka kashe mai suna Tukur Kurma yana karantar da bangaren tarihi ne a makarantar sakandaren gwamnati na Gummi

Zamfara - Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun bindige wani malamin makarantar sakandare har lahira a jihar Zamfara, TVC News ta rahoto.

An bindige malamin makarantar mai suna Tukur Kurma a lokacin da yan bindigar suka bude wuta kan matafiya a hanyar Tashar Taya, yankin Danzaurfe da ke babban titin Anka-Dakitwakwas-Gummi a yammacin ranar Talata, 19 ga watan Afrilu.

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun kashe wani malamin sakandare a Zamfara
Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun kashe wani malamin sakandare a Zamfara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan bindigar sun harbi motar mai tafiya a lokacin da direban ya ki tsayawa tare da wasu ababen hawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bindige sabon zababben kansilan APC a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2

Marigayi Kurma ya kasance babban malamin tarihi a makarantar sakandaren gwamnati na Gummi da ke jihar Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kawo cewa lamarin na zuwa ne kwanaki hudu bayan yan bindiga sun kashe mutane hudu a Musamar Mudi, wani gari a karamar hukumar Bukkuyum da ke jihar.

Daga Zuwa Daurin Aure, Ƴan Bindiga Sun Sace Baƙi Guda 5 a Hanyarsu Ta Komawa Gida

A wani labarin kuma, mun ji cewa a kalla mutane biyar ne cikin baki da suke dawowa daga bikin daurin aure na gargajiya a Anambra a daren ranar Litinin ne suka fada hannun yan bindiga, rahoton Daily Trust.

DSP Toochukwu Ikenga, Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Anambra, ya tabbatar da afkuwar wannan lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya a Awka.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 5 a Hanyarsu Ta Dawowa Daga Ɗaurin Aure

The Cable ta rahoto cewa Ikenga ya ce yan sanda sun bazama don ceto wadanda aka sace a kuma sada su da iyalansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel