Kano: Kwamishinan Da Ganduje Ya Ce Kada Ya Ajiye Aiki Ya Bijire Wa Umurnin, Ya Yi Murabus Ya Yi Tafiyarsa

Kano: Kwamishinan Da Ganduje Ya Ce Kada Ya Ajiye Aiki Ya Bijire Wa Umurnin, Ya Yi Murabus Ya Yi Tafiyarsa

  • Nura Muhammad Dankadai, Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kudi na Jihar Kano ya ajiye aikinsa ya mika mulki ga Sakataren Dindindin na ma'aikatar
  • Hakan na zuwa ne duk da cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya umurci shi da wasu kwamishinoni biyu su cigaba da aiki
  • Kakakin Ma'aikatan Kasafin Kudin, Sulaiman Dederi ya tabbatar da murabus din yana mai cewa tsohon kwamishinan ya ce ya kammala aikinsa don haka ba shi da ra'ayin cigaba

Jihar Kano - Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kudi na Jihar Kano, Nura Muhammad Dankadai, ya mika murabus dinsa, sabanin umurnin da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar ya bada, rahoton Daily Trust.

Dankadai yana daya daga cikin kwamishinoni uku da Ganduje ya basu umurnin kada su ajiye aikinsu.

Kara karanta wannan

Niger: An Yanke Wutar Lantarki a Ofisoshin Gwamnati Kan Bashi Da Aka Tara Tsawon Shekaru 8

Kano: Kwamishinan Da Ganduje Ya Ce Kada Ya Ajiye Aiki Ya Bijire Wa Umurnin, Ya Yi Murabus Ya Yi Tafiyarsa
Kwamishinan Da Ganduje Ya Ce Kada Ya Ajiye Aiki Ya Bijire Wa Umurnin, Ya Yi Murabus Ya Yi Tafiyarsa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Depositphotos

Kwamishinoni bakwai ne suka bayyana niyyarsu na ajiye aiki domin za su yi takara a zaben shekarar 2023 da ke tafe.

Yayin da gwamnan ya amince da murabus din hudu cikinsu, ya umurci uku ciki har da Dankadai su cigaba da aiki.

Amma, Dankadai, ya saba umurnin ya mika mulkin ma'aikatan ga sakataren dindindin, Alhaji Auwalu Umar Sanda, a ranar Laraba.

Kakakin Tsare-Tsare da Kasafin Kudi na Jihar Kano Ya Magantu Kan Murabus Din

Kakakin Ma'aikatan, Sulaiman A. Dederi, ya tabbatar da hakan cikin wata takarda da ya fitar bayan bikin mika mulkin, yana mai cewa:

"Sakataren na dindindin, yayin karbar mulkin, ya mika godiya ga kwamishina mai barin gado da dukkan ma'aikata bisa jajircewarsu, kuma ya yi alkawarin aiki tare da dukkansu don cimma manufar ma'aikatar."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: N100m zamu sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC

A yayin da Daily Trust ta tuntubi kakakin ya yi tsokaci bisa umurnin gwamnan, ya ce kwamishinan ya yanke shawarar ajiye aiki ne duk da gwamnan ya ki karbar murabus dinsa.

"Kwamishinan ya ce ba zai cigaba da aiki ba kuma ya ki amincewa da abin da gwamnan ya ce. Ya ce ya kammala aiki a matsayin kwamishina kuma ba zai dawo ba. Hakan yasa ya mika wa sakataren dindindin," in ji Dederi.

Dankadai na da niyyar yin takarar dan majalisar wakilai na tarayya

Daily Trust ta rahoto cewa Dankadai na da niyyar dare wa kujerar dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Doguwa/Tudunwada, Alhassan Ado Doguwa.

Doguwa na hannun daman gwamnan Jihar ne.

Yahaya Bello: Ƙaruwar Masu Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa Baya Bani Tsoro Ko Kaɗan

A bangare guda, dan takarar shugaban kasa kuma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce ko fargaba ba ya yi akan yadda mutane da dama suke ta fitowa takarar shugaban kasa, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci ke raba kan 'ya'yan jam'iyya, Abdullahi Adamu

Haka zalika, ya ce bai tsorata ba da shirye-shiryen yarjejeniyar jam’iyya ba saboda yana sa ran kasancewa mai nasara a ko wanne irin mataki jam’iyyar ta dauka wurin zaben dan takara.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Kungiyar Kamfen din shugabancin kasar Yahaya Bello ta shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel