Niger: An Yanke Wutar Lantarki a Ofisoshin Gwamnati Kan Bashi Da Aka Tara Tsawon Shekaru 8

Niger: An Yanke Wutar Lantarki a Ofisoshin Gwamnati Kan Bashi Da Aka Tara Tsawon Shekaru 8

  • Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC, ta yanke wutar lantarki a wasu ofisohin gwamnatin Jihar Niger kan rashin biyan kudin wata
  • Hukumar ta ce tana bin bashin kudi da ya kai Naira Biliyan 1.9 da ya taru cikin shekaru takwas, kuma babu alamar za a biya ta
  • Ofishoshin da aka yanke wa wutan sun hada da Majalisar Dokokin Jihar, Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Hukumar Ruwan Fanfo da wasu

Minna, Niger - Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC, ta fara yanke wutar lantarki a ofisoshin gwamnati a Jihar Niger saboda bashin da ta ke bi da ya kai Naira Biliyan 1.9.

Ofisoshin da aka yanke wutarsu kawo yanzu sun hada da na Majalisar Dokokin Jihar, Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar, Hukumar Ruwan Fanfo da sauransu.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Ofishin Babban Bankin Najeriya, CBN, Ta Kama Da Wuta

Niger: An Yanke Wutar Lantarki a Ofisoshin Gwamnati Kan Bashi Da Aka Tara Tsawon Shekaru 8
An Yanke Wutar Lantarki a Ofisoshin Gwamnatin Jihar Niger Kan Bashin N1.9bn. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Daily Trust ta gano cewa an kunna injin janareta ne a ofisoshin Majalisar Dokokin Jihar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar a yayin da ma'aikata ke dawowa daga hutun Easter.

Wata sanarwa da babban manajan yankin Minna na AEDC ya fitar a ranar Juma'a ta ce tsawon shekaru takwas ake bin bashin, kuma ya sha alwashin ba zai mayar da wutar ba sai an biya su, LIB ta rahoto.

Sanarwar ta ce gwamnatin baya-baya na jihar ta bar bashin Naira Miliyan 343, sannan daga Yunin 2015 zuwa yanzu, bashin ya kai Naira Biliyan 1.9.

Ta kuma ce an yi kokarin ganin an biya bashin amma hakan ya ci tura.

Gwamnati Ta Rufe Ofishin Hukumar Lantarki Saboda Yanke Wutar Ofishin Gwamna

Kara karanta wannan

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Mohammed Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani labarin, Hukumar rarraba wutar lantarki na Ibadan, IBDEC, ta ce Gwamnatin Jihar Oyo, ba bisa ka'ida ba, ta rufe mata ofisohinta saboda yanke wutar lantarki na Sakatariyar Jihar wanda ke hade da Ofishin Gwamna, rahoton Punch.

Kamfanin lantarkin ta ce tana bin gwamnatin jihar bashin Naira miliyan 450 hakan yasa ta yanke wutar sakatariyar don ba a biya bashin ba amma gwamnatin jihar sai ta mayar da martani ta hanyar rufe ofisoshinta da sunan ana binsu bashi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kamfanin, John Ayodele, a ranar Laraba, da mai magana da yawun hukumar IBEDC, Busolami Tunwase ya fitar.

Mazauna garin Minna da yanke wutar Water Board ya shafa sun koka

Wasu mazauna garin Minna sun magantu kan irin mawuyancin halin da yanke wutar Hukumar Ruwa ta Water Board ya jefa su ciki.

Wata matar aure da ke zaune a unguwar Farm Centre, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta shaidawa Legit.ng Hausa cewa rashin ruwan ya sanya masu baru sun tsawalla kudin ruwa ya kai N1000 duk baro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fara rabon ton 40,000 na hatsi don Easter da Azumi ga talakawa

"Yanzu haka duk lamarin ya shafemu mu mazauna garin Minna sakamakon yanke wutan Water Board tun shekaran jiya babu ruwa ga masu ruwan baro kasuwa ta bude masu N1000 suke siyar da baro daya," in ji ta.

Ta yi fatan a za a wareware matsalar cikin gaggawa domin al'umma su cigaba da samun ruwa musamman a yanayi irin na azumi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel