Daga Zuwa Daurin Aure, Ƴan Bindiga Sun Sace Baƙi Guda 5 a Hanyarsu Ta Komawa Gida
- 'Yan bindiga sun sace mutane biyar cikin baki da suka tafi wurin bikin daurin aure a karamar hukumar Aguata da ke Jihar Anambra
- Wata majiya kwakwara ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa maharan sun tare su a hanya ne suka dibi maza suka saki mata
- Rundunar yan sandan Jihar Anambra ta bakin kakakinta Toochukwu Ikenga ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ta ce tana aikin ceto su
Jihar Anambra - A kalla mutane biyar ne cikin baki da suke dawowa daga bikin daurin aure na gargajiya a Anambra a daren ranar Litinin ne suka fada hannun yan bindiga, rahoton Daily Trust.
DSP Toochukwu Ikenga, Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Anambra, ya tabbatar da afkuwar wannan lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya a Awka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Cable ta rahoto cewa Ikenga ya ce yan sanda sun bazama don ceto wadanda aka sace a kuma sada su da iyalansu.
Wata kwakwarar majiya ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa, NAN, cewa an sace bakin ne misalin karfe 10 na dare a hanyarsu ta komawa gida.
"Bakin da aka sakaya sunansu, an sace su ne misalin karfe 10 na dare a hanyar Akpo-Nkpologwu a karamar hukumar Aguata a Jihar Anambra.
"Kimanin bakin su 15 ne ke komawa otel dinsu daga Achina, inda aka yi auren sai tawagar motocinsu ta fada hannun yan bindiga, amma motar farkon kawai ta tsere.
"Yan bindigan sun umurci dukkan matan su tafi amma suka sace maza biyar suka tafi suna harbe-harbe," a cewar majiyar.
Ta kara da cewa kawo yanzu ba su tuntubi yan uwan wadanda suka sace din ba.
'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda
A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.
Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.
Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng