A Yayin Da Ortom Ya Yabi Buhari, Wike Ya Masa Kaca-Kaca Kan Yi Wa Dariye Da Nyame Afuwa

A Yayin Da Ortom Ya Yabi Buhari, Wike Ya Masa Kaca-Kaca Kan Yi Wa Dariye Da Nyame Afuwa

  • Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya caccaki Gwamnatin Tarayya akan yafe wa tsohon Gwamnan Jihar Filato, Joshua Dariye da na Jihar Taraba, Jolly Nyame bayan daure su akan rashawa
  • Wike, wanda dan takarar shugaban kasa ne karkashin jam’iyyar PDP ya ce yafiyar da gwamnati ta yi musu na nuna cewa duk siyasa ne batun yaki da rashawar da take yi
  • Gwamnan ya yi wadannan furucin ne a ranar Asabar yayin da ya kai ziyarar kamfen Jihar Neja, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar yake ta karatowa

Niger - Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya caccaki Gwamnatin Tarayya akan yafe wa tsohon Gwamnan Jihar Filato da na Jihar Taraba, Joshua Dariye da Jolly Nyame, wadanda aka daure akan rashawa, rahoton The Punch.

Wike, wanda dan takarar shugaban kasa ne na PDP, ya ce afuwar alama ce da ke nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta raina wa ‘yan Najeriya hankali kuma siyasa kawai take yi ba yaki da rashawa ba.

Kara karanta wannan

Nayi matukar farin cikin yafewa Dariye da Nyame, Buhari ya amsa kira na: Jonah Jang

A Yayin Da Ortom Ya Yabi Buhari, Wike Ya Masa Kaca-Kaca Kan Yi Wa Dariye Da Nyame Afuwa
Wike Ya Ti Wa Buhari Kaca-Kaca Kan Yi Wa Dariye Da Nyame Afuwa. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Wike ya yi wannan maganar ne yayin da ya kai ziyara wani yanki na Jihar Neja don kamfen ga wakilan jam’iyyar PDP sakamakon yadda zaben fidda gwani yake kara matsowa.

Gwamnan ya ce abu mai wahala ne a yi bayani akan dabarar Gwamnatin Tarayya ta zaben wadanda suka aikata rashawa, kotun koli ta hukunta su sannan a dawo ta sake su a matsayin yafiya.

A wata takarda wacce hadiminsa na musamman na bangarem watsa labarai ya saki, Wike ya bayyana yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yaki da rashawa.

Ya ce saboda siyasa ne aka sako Dariye da Nyame

A cewarsa Buhari yana yin hukunci ne da wadanda ba su da amfani ga gwamnatinsa a siyasance kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Zan Cigaba Daga Inda Jonathan Ya Tsaya, In Ji Ɗan Takarar Shugaban Kasa A PDP

Kamar yadda ya ce:

“In fada muku gaskiya, wannan gwamnatin ta APC ta yaudarmu kwarai. Gwamnatin ta ce tana yaki da rashawa amma zaben mutane take yi ta dauresu bayan sun gama shari’a a kotun koli.
“Daga bisani kuma sai su saki mutanen da ke gidan yari wadanda suka ce duk ‘yan rashawa ne. Wacce irin gwamnati ko kuma kasa ce wannan?
“Sun yi hakan ne don siyasa, zabe ya kusa zuwa kuma suna son Dariye ya taimaki jam’iyyarsu a Jihar Filato. Sannan suna bukatar taimakon Nyame a Jihar Taraba. Me ya hana su yafe wa James Ibori, misali.”

Ya ce shi ne zai kawo karshen karairayin da APC ta yi wa ‘yan Najeriya

Ya ci gaba da cewa sun ja EFCC ta yi asarar makudan mudade wurin shari’a da su. Daga baya kuma sun mayar da abin siyasa. Da wanne ido suke son jama’an kasashen waje su kalli Najeriya? Ai wannan abin kunya ne, in ji Wike.

Kara karanta wannan

2023: Kwankwaso Ya Bayyana Lokacin Da Zai Ƙaddamar Da Takararsa Na Shugabancin Ƙasa

Ya sanar da wakilan cewa shi ne zai kawo karshen karairayin da APC ta ke yi wa ‘yan Najeriya, hakan yasa ya ke ta kokarin neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Ya yi alkawarin yaki da rashin tsaron da ya addabi yankuna daban-daban na kasar nan don manoma su koma noma a gonakinsu sannan tattalin arzikin kasa ya karu.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel