Wai Kana Da Gida A Landan Ne? Sarkin Ingila Ya tambayi Buhari

Wai Kana Da Gida A Landan Ne? Sarkin Ingila Ya tambayi Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sha tambaya hannun sabon Sarkin Ingila, King Charles Na Uku
  • Wannan shine karo na farko da Shugabannin biyu zasu hadu tun bayan mutuwar mahaifiyar Sarkin
  • Shugaba Buhari ya tafi birnin Landan hutu da ganin Likitansa kuma zai kwashe makonni biyu

Sarkin Ingila, Mai Martaba Charles III ya karbi bakuncin shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ranar Laraba.

Shugaba Buhari ya ce ya kaiwa Sarkin ziyara ne domin inganta alakar diflomasiyyar dake tsakanin Najeriya da Birtaniya.

A tattaunawar da sukayi, Sarkin na Ingila ya tambayi Shugaba Buhari shin yana da gida a Ingila.

Buhari da kansa ya bayyana hakan a hirar da yayi da tashar NTA bayan ganawarsa da Sarkin

Buhari
Wai Kana Da Gida A Landan Ne? Sarkin Ingila Ya tambayi Buhari Hoto: @BuhariSallau
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Akan Sauya Fasalin Naira, Ba Zamu Fasa Ba: Shugaba Buhari Ya Bayyana A Landan

Yace:

"Ya tambayeni shin ina da gida a nan ne (Birtaniya), sai nace masa a'a. A Najeriya kadai nike zama. Kuma gidajen da nike da su a can ma tun kan na hau mulki na mallakesu."
"Ba na bukatar mallakar gidaje a ko ina. Na fi samun kwanciyan hankali idan ban da komai."

Kalli bidiyon:

Dalilin ziyararsa

Game da dalilin ziyarar da ya kaiwa Sarkin an Ingila, Buhari yace Najeriya na bukatar masu sanya hannun jari daga kasar Birtaniya.

Yace:

"Na farko, ya kamata ace mun hadu a Kigali amma sai aka dage taron. Yana da matukar ra'ayin Najeriya, la'alla ko dan alakar Najerya da Birtaniya na da tsawo."
"Ya yi kalamai masu kyau kan Najeriya kuma yana son alakarmu ta cigaba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel