Ku kawo fansa ko mu kashe sauran: 'Yan bindiga sun hallaka mutum 3 da suka sace a Kaduna
- Yan bindiga sun kashe mutum uku daga cikin 26 da suka sace a garin Unguwan Bulus da ke jihar Kaduna
- Wadanda suka yi garkuwa da mutanen sun kuma yi barzanar kashe sauran mutane da ke hannunsu idan har ba a biya kudin fansa ba
- Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna ya tabbatar da lamarin, ya ce suna kokarin ganin mutanen sun dawo lafiya
Kaduna - Yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu mutane a Anguwan Bulus da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna sun kashe uku daga cikin su sannan sun yi barazanar kashe wasu har sai an biya kudin fansa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kakakin yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da kisan yana mai cewa:
“Na amsa kiran waya daga wasu mutane uku a safiyar nan cewa an tsinci gawarwakin mutum uku a kauyen Dutse a wani waje a cikin jeji. An kwashe gawarwakin zuwa asibitin Saint Gerald Hospital. Muna kokarin tattaunawa da kwamandan yankin domin tabbatar da ganin wadanda ke tsare sun dawo lafiya."
Jaridar The Guardian ta kuma rahoto cewa babban basaraken Unguwan Bulus, Gideon Haruna Goni, ma ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a lokacin da suka ziyarci fadarsa a ranar Talata.
An tattaro cewa kimanin makonni biyu da suka gabata, yan bindiga sun farmaki garin Anguwan Bulus inda suka kashe mutum daya tare da sace wasu da dama.
Hakazalika sun farmaki garuruwan da ke makwabta irin su Juji, Angwan Gimbiya da Sabo GRA.
Wata majiya ta ce:
“Yan bindigar sun kira lambar garinsu cewa su je wani wuri a kauyen Dutse hanyar titin Kaduna zuwa Abuja don daukar gawarwakin mutane uku da suka kashe saboda rashin biyan kudin fansa. Yan bindigar sun kira jiya cewa sun kashe mutum uku da suka sace sannan sun fada mana inda aka ajiye gawarwakinsu."
Harin jirgin Abj-Kad: FG ta ki yarda da bukatar sakin kwamandojin 'yan bindiga kafin sako wadanda aka sace
Wata majiya ta kuma ce:
“Yan ta’addan sun kira a yammacin jiya sannan sun ce tunda mun ki biyan kudin fansa, to mu je wani waje sannan mu dauki gawarwakin mutanenmu.
“A yanzu haka, mun shiga rudani. Ba mu san abun yi ba. Mun siyar da duk abubuwan da muka tara don lallashin mutanen nan amma suna so mu karo. Muna rokon gwamnatocin tarayya da jiha da su kawo mana dauki don ceto sauran mutanenmu da ke tsare.”
An Tsinci Gawar Ɗan Kasuwar Kano Bayan Iyalansa Sun Biya N6m Ga Masu Garkuwa
A wani labarin, iyalan Yahaya Hassan Musa, dan kasuwa mai shekaru 39, sun shiga zaman makoki bayan an gano gawarsa a wani daji awanni bayan wadanda suka sace shi sun karbi Naira miliyan 6 matsayin kudin fansa, rahoton Daily Trust.
Lamarin ya samo asali ne a ranar Alhamis, a yayin da mutum wanda ke da aure da 'ya'ya biyu, ke dawowa daga Cotonou, inda ya tafi kasuwanci amma aka sace shi a wani daji da ke Mopa, Jihar Kogi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa da farko masu garkuwan sun nemi a biya su Naira miliyan 10 domin fansarsa daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 6.
Asali: Legit.ng