Kaduna: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun halaka mutum 2 tare da jigata wasu

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun halaka mutum 2 tare da jigata wasu

  • 'Yan ta'adda sun kai mummunan farmaki yankin Agban Kagoro da ke karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna
  • Ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar kuma miyagun sun halaka rayuka 2 tare da jigata wasu
  • Tsohon shugaban karamar hukumar Kaura, Kumai Badu ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace an mika wadanda suka samu rauni asibiti

Kaura, Kaduna - A ranar Asabar da ta gabata ne miyagun 'yan ta'adda suka tsinkayi karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna inda suka halaka mutum biyu, jaridar Punch ta ruwaito hakan.

Karamar hukumar Kaura tana karkashin yankin Kudancin jihar Kaduna.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun halaka mutum 2 tare da jigata wasu
Kaduna: 'Yan bindiga sun kai sabon hari, sun halaka mutum 2 tare da jigata wasu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya daga yankin mai suna Christopher Derek ya sanar da The Nation cewa 'yan bindiga sun halaka rayukan mutum biyu tare da raunata wasu.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, tsohon shugaban karamar hukumar Kaura, Kumai Badu, ya ce wadanda aka raunata an kai su asibiti.

Wannan farmakin na zuwa ne kasa da wata daya bayan makamancinsa ya faru a yankuna biyu na karamar hukumar inda aka rasa rayuka 34 tare da barnatar da dukiyoyin miliyoyin kudi.

Ba a riga an samu kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, a waya ba domin jin ta bakinsa kafin rubuta wannan rahoton.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 11

A wani labari na daban, a kalla sojoji 11 ne aka kashe a mugun hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda majiya ta shaida wa TheCable.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari Gonar Gidan Yari, Sun Kashe Mutum Ɗaya, Sun Sace Dabobbi Masu Yawa

‘Yan bindigar da suka isa sansanin da yawansu sun kutsa cikin sansanin da ke kauyen Polwire a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi artabu da sojojin.

Majiyar soji ta shaida wa jaridar TheCable cewa, ‘yan bindigar sun bayyana a kan babura kuma suna dauke da manyan makamai da suka hada da gurneti (RPG).

An sanar da cewa an dauki kimanin sa'o'i biyu ana gwabza fada kafin a fatattaki 'yan ta'addan.

“Mun yi asarar sojoji 11 yayin da sojoji 19 suka samu miyagun raunuka, bayan da 'yan ta'addan suka far wa sojojin. Hakazalika sun kona motocin yaki masu sulke (APC) guda uku,” in ji wata majiya daga sojojin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng