Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Allah ya yiwa mahaifiyar Dadiyata rasuwa

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Allah ya yiwa mahaifiyar Dadiyata rasuwa

  • Allah ya yiwa Malama Fatima, mahaifiyar Abubakar Idris Dadiyata wanda wasu da ba a san ko su waye ba suka sace shi, rasuwa
  • Marigayiyar ta amsa kiran mahaliccinta ne a safiyar yau Talata, 19 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da rashin lafiya
  • Wasu makusanta da abokan Dadiyata sun tabbatar da labarin mutuwar tata a shafukansu na sadarwa

Kaduna - Labari da ke zuwa mana shine cewa Allah ya yiwa Malama Fatima, mahaifiyar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, rasuwa.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa Malama Fatima ta rasu ne a safiyar yau Talata, 19 ga watan Afrilu, bayan ta yi fama da jinya a asibitin sojoji na 44 da ke jihar Kaduna.

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Allah ya yiwa mahaifiyar Dadiyata rasuwa
Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Allah ya yiwa mahaifiyar Dadiyata rasuwa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoton ya kuma kawo cewa wani makusancin iyalan, Lawal Muhammad, ya tabbatar da cewar an garzaya da marigayiyar zuwa asibiti ne da asubahin yau sakamakon tsanani da jikin nata ya yi.

Kara karanta wannan

Babu baraka a kungiyar dattawan arewa, muna biyayya ga Ango Abdullahi – Baba Ahmed

Malam Lawal wanda ya kasance amini ga yayan Dadiyata, Usman Idris, ya ce a yanzu haka, abokin nasa na a hanyarsa ta komawa Kaduna, bayan ya samu labarin rasuwar mahaifiyar tasu.

Wani abokin Dadiyata mai suna Ibrahim Adam ya sanar da labarin mutuwar a shafinsa na Twitter yana mai cewa:

“Mutuwa ta dauke mahaifiyar abokinmu Dadiyata da ya bata. Allah ya ji kanta.”

Nasiru Fulatan @nkfulatan ya rubuta a shafinsa:

"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! Dan uwanmu kuma abokinmu da aka sace Abubakar Idris Dadiyata ya rasa mahaifiyarsa a yau. Ina mika ta’aziyyata ga iyalansu baki daya. Allah ya basu juriyar daukar wannan rashi Allah ya mata rahama!"

Legit Hausa ta nemi jin ta bakin wani abokin Dadiyata mai suna Mallam Malumfashi inda ya nuna alhini tare da addu'an Allah ya bayyana abokin nasa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Ya ce:

“InnalilLahi wa inna ilaihi rajiun!!! Allah ya isa!! Allah ya yafe mata. Allah bayyana shi."

A ranar 2 ga watan Agusta, 2019, ne wasu mutane da har yau ba a san su wanene ba, suka dauke wannan matashi da ake kira Dadiyata, har yau babu labarinsa.

Dadiyata wanda malamin makaranta ne ya bar iyalinsa da 'ya 'ya biyu.

Martanin Dan uwan Dadiyata

Legit Hausa ta zanta da kanin Dadiyata mai suna Mallam Usman inda ta nemi jin ko batansa yana da nasaba da rashin lafiyar mahaifiyarsu sai ya ce dama tana da hawan jini amma faruwar lamarin ya sa yana tayar mata lokaci zuwa lokaci.

Usman ya ce:

“Gaskiya tun kafin batar Dadiyata tana da hawan jini, amma kusan da abun ya faru mun yi kokari wajen ganin mun kwantar mata da hankali, don gaskiya ni abun da ya fara zuwa raina kenan. Na ce mata dan Allah ta yi hakuri wannan abun da ya faru batar Dadi abun bakin ciki ne amma duba da yanayin da take ciki, kada ta daga hankalinta yadda ciwonta zai zo ya tashi, yadda abun zai zama mana gida biyu.

Kara karanta wannan

Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya

“Tun a lokacin dai da taimakon Allah ta samu nutsuwa, ta ci gaba da harkokinta, lokaci-lokaci ka san uwa da ‘da abun zai motso mata haka sai ta fara kunci da bacin rai ka ga abun ya dan motsa, tana shan magungunanta abun zai lafa haka.
“Akwai wani biki da aka yi na wata yaruwarmu bayan batan shi Dadi din, kusan ana cikin harkoki da ta shiga uwardaka tana shiryawa, ta sa kayan biki komai kawai sai na shiga na tarar da ita a zaune ta fashe da kuka, nace mama mai ya faru? Sai ta ce Dadi, kawai shi ya fado mata a rai, ga shi ana ta sha’ani ga yan’uwa ga kowa amma Dadiyata baya wajen.
“Sai nace mama eh kiyi hakuri, kuma ana iya abin da za a yi idan Allah ya yarda Dadi zai dawo cikinmu ko bajima ko badade. Sai muka samu muka kwantar mata da hankali, muka ce kina tunanin kin gayyato mutane aga kin fito kina kuka me aka yi?, na tuna wannan ya zo ya wuce.

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

“Tun lokacin Allah ya saukar mata da nutsuwa gaskiya, don wasu idan suka shigo gidan nan ma ba za su ce itace mahaifiyar Dadiyata ba. Amma lokaci-lokaci idan abun ya motso mata duk inda ta zauna za ka ga kamar idonta ya taru da kwalla toh da na ga haka sai wannan ne. Ta kan ce toh bamu sani ba ko za mu gana ko ba za mu gana ba, sai nace mata in shaa Allahu ma za ku gana.
“Toh a zahirin gaskiya tana da wannan ciwon kafin a sace shi amma faruwar abun ya sa lokaci-lokaci abun yana tayar mata. Toh amma haka aka yi ta fama har zuwa lokacin da Allah ya yi ikon shi.”

Kungiya ta bukaci Gwamnatin Buhari ta binciki bacewar Dadiyata bayan kwanaki 761

A wani labarin, mun ji a baya cewa wata kungiya ta Access to Justice (A2Justice) ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciki lamarin bacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

Kara karanta wannan

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

Kungiyar A2Justice ta yi magana a game da bacewar wannan Bawan Allah ne yayin da ake bikin tuna wa da mutanen da suka bace a duk kasashen Duniya.

A ranar 30 ga watan Agustan kowace shekara ake tuna wa da mutanen da aka nema aka rasa – a dalilin dauke su, tsare su ko kuma a tauye masu hakkinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel