Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya

Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya

  • An yi kira muhimmi ga 'yan Najeriya masu hanyoyin wuff da matan marigariyi Alaafin na Oyo da su dakata kada su kusanto su
  • Kamar yadda Chief Ifayeki Elebuibon ya ce, akwai wasu abubuwan al'adun da sai an yi kafin matan su iya rayuwa da wasu maza
  • Haka zalika, ya kara da cewa idan sarki ya mutu ya bar mata a fadarsa, akwai yuwuwar wani sarkin ya yi wuff da su idan matan sun amince

Oyo, Ibadan - Ba sabon labari bane idan ance Oba Lamidi Adeyemi lll, Alaafin na Oyo ya mutu bayan shekaru 52 a karagar mulki, da kuma yaduwar batun mutuwarsa musamman a kafafan sada zumuntar zamani,

Oba Adeyemi mai shekaru 83 ya bar gidan duniya a daren Juma'a bayan jinyar da ya sha a asibitin Afe Babalola dake Ado Ekiti.

Kara karanta wannan

Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa

Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya
Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya. Hoto daga @authenticvoice
Asali: Twitter

Sai dai an ce da 'yan Najeriyan da suka hango yin wuff da matan marigayin basarake da su dakata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Oba Lamidi na matukar kaunar mata, musamman kyawawa masu jini a jika, bai taba boye wannan batun ba.

Hotunan basaraken da matan nasa ya yadu a kowacce kafar sada zumuntar zamani.

A tattaunawar da BBC Yoruba tayi da Chief Ifayeki Elebuibon ya bukaci mazan dake hararo matan sarkin da su kara hakuri. A cewarsa, har yanzu matan na takaba.

Ya ce, ba me iya aurensu har sai sun gama takabar marigayin basaraken, kuma babban abu ma, har sai an fitar dasu daga takaba a al'adance.

Matan marigayin sarkin na da damar auren duk wanda suka ga dama, amma dole sai annbi matakan da al'ada ta tanada kafin su auru.

Bayan an cire musu kafin da Alaafin din ya musu. Daga nan ne za su jira sabon sarki. Idan sabon sarkin na da ra'ayin zama dabsu, zai cigaba da zama mijinsu.

Kara karanta wannan

Matar da ta fi kowacce mace kudi a Najeriya ta bukaci mata da su mika wuya ga mazajensu

"A koda yaushe sarakuna na barin sarauniyoyi a fada bayan sun mutu," a cewarsa.

Ya kara da cewa, a halin yanzu, kada wanda ya yi gigin zuwa kusa da matan sarkin.

Allah ya yi min baiwar auren kyawawan mata, Salon sace zuciyar 'yan mata daga bakin Alaafin yayin rayuwarsa

A wani labari na daban, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi lll, ya riski magabatansa a daren Juma'a, wanda hakan ya kawo karshen shekaru 52 da ya yi a karagar mulki.

Oba Adeyemi, mai shekaru 83, wanda ya rasu a asibitin koyarwa na jami'ar Afe Babalola na Ado Ekiti dake jihar Ekiti, shine Alafin na Oyo da yafi kowanne basarake dadewa a karagar mulki.

Ya rasu ya bar mata 11, uwar gidan mai suna Ayaba Abibat Adeyemi, wacce yafi zuwa da ita taruka ko daya daga cikin sauran matayen nashi guda goma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel