Kungiya ta bukaci Gwamnatin Buhari ta binciki bacewar Dadiyata bayan kwanaki 761

Kungiya ta bukaci Gwamnatin Buhari ta binciki bacewar Dadiyata bayan kwanaki 761

  • Kungiyar Access to Justice ta tabo batun Dadiyata da ya bace tun a Agustan 2019
  • A2Justice ta yi bikin tuna wa da mutanen da aka nema aka rasa a Najeriya a jiya
  • Shekaru biyu da suka wuce aka je gida aka dauke Dadiyata, har yau babu labari

Wata kungiya ta Access to Justice (A2Justice) ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta binciki lamarin bacewar Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.

Kungiyar A2Justice ta yi magana a game da bacewar wannan Bawan Allah ne yayin da ake bikin tuna wa da mutanen da suka bace a duk kasashen Duniya.

A ranar 30 ga watan Agustan kowace shekara ake tuna wa da mutanen da aka nema aka rasa – a dalilin dauke su, tsare su ko kuma a tauye masu hakkinsu.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Mun taba yi wa mutum 76 jana’iza a lokaci guda, babu wanda ya ji labari inji Sultan

Najeriya ta na cikin kasashen da jami’an tsaro da ‘yan bindiga suka saba tsare mutum, a daina ganinsa, don haka ake yin wannan biki a rana irin ta jiya.

A wani jawabi da A2Justice ta fitar a ranar Litinin, ta yi kira ga jami’an tsaro su girmama hakkin Bil Adama a kasar nan, su fito da duk wadanda suke tsare.

A2Justice ta ce bacewar Abubakar Idris a Agustan 2019 ya jefa masoyansa a cikin takaici, zulumi da dar-dar. Jaridar The Cable ce ta fitar da wannan rahoto.

Dadiyata
Abubakar Idris Dadiyata Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“Yayin da aka gano inda Gloria ta ke, ba haka lamarin yake ga Dadiyata ba. A watan Agustan shekarar 2021 aka cika shekara biyu da bacewarsa.”
“Shekara biyu ana cikin rashin tabbas, babu kwanciyar hankali, ga zulumi ga abokansa da ‘yanuwa.”

Kara karanta wannan

Kotu ta tsare mutane 8 da ake zargi da yin garkuwa da matar kwamishinan Benue

“Wannan shi ne batar da mutane; makasudin hakan shi ne jawo tsoro da firgici a al’umma. Gloria Okolie da Abubakar Idris suna cikin jerin dinbin mutanen da suka bace. Ana hasashen dubunnai sun bace da son ronsu, ko ba da son ransu ba a kasar.”

Wannan kungiya ta yi kira ga gwamnati ta yi bincike tukuru a kan duk wadanda aka nema aka rasa, domin a tabbatar an yi wa wadannan mutanen adalci.

Shekara biyu kenan

A ranar 2 ga watan Agusta, 2019, wasu mutane da har yau ba a san su wanene ba, suka dauke wannan matashi da ake kira Dadiyata, har yau babu labarinsa.

Iyaye da iyali sun koka game da halin tashin hankalin da suka shiga a shekaru biyu. Dadiyata wanda malamin makaranta ne ya bar iyalinsa da 'ya 'ya biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel