Bana 'yan crypto za su kudance: CEO a crypto ya yi hasashe, farashin bitcoin zai kai N41m

Bana 'yan crypto za su kudance: CEO a crypto ya yi hasashe, farashin bitcoin zai kai N41m

  • Babban tsaban crypto mafi daraja, bitcoin zai kai $100,000 a cikin watanni 12 a cewar wani Shugabana wani kamfanin crypto
  • Shugaban na Nexo ya ce bitcoin ya gama haurawa sama a baya, amma akwai yiwuwar shirin da gwamnatin Amurka ta gabatar ya iya tasiri kan farashinsa yanzu
  • Antoni Trenchev ya yi hasashen hawan farashin bitcoin sama da $50,000 a cikin 2020 wanda ya faru a watan Janairun bara (2021)

An yi hasashen cewa, kudi mafi daraja a kasuwar crypto wato bitcoin zai haura zuwa kusan Naira miliyan 41.2 (dalar Amurka 100,000) a cikin shekara guda, a cewar shugaban kamfanin Nexo, wani babban kamfani na crypto a duniya.

A wata hira da CNBC, Antoni Trenchev ya ce ya yi imani da cewa, bitcoin zai iya tashi sama da $100,000 a cikin watanni 12.

Kara karanta wannan

Mai neman Shugaban kasa ya ce Najeriya za tayi takara da Amurka idan ya samu mulki

Farashin kayan crypto zai tashi nan kusa
Bana 'yan crypto za su more: CEO a crypto ya yi hasashe, farashin bitcoin zai kai N41m | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

Bitcoin zai ninka a farashinsa nan ba da jimawa ba

A cewarsa, ya damu matuka game da makomar bitcoin a cikin gajeren lokaci yayin da babban bankin Amurka, wanda yake daidai da CBN na Najeriya, ya fara kaddamar da wani shirin da zai sa crypto ya fadi ya tafi daidai da kasuwanni na yau da kullum.

Amma ya kara da cewa shirin na kasar Amurka kuma zai iya ba da kuzari ga farashin bitcoin a duniya.

Wannan yana nufin cewa farashin bitcoin zai iya shillawa sama fiye da ninki biyu a wannan shekara, idan zaton tsinkayar Trenchev ta zama daidai.

Ya yi hasashe a watan Janairu cewa farashin bitcoin zai kai dala 50,000 a karshen shekarar 2022. Ya ce mutane sun sha yi masa masa ba'a kan hasashen nasa.

Kara karanta wannan

Bala Mohammed: Buhari ya yi rugu-rugu da Najeriya amma ni zan gyara ta

Kwararru sun fara kwasar bitcoin a kasuwa

Hasashen da Trenchev ya yi a 2020 bai cika ba, duk da cewa bitcoin ya kai $29,000 a waccan shekarar sai kuma a karshe ya haura sama da $50,000 a cikin Fabrairun 2021.

Masu sa ido na Crypto sun ce kasuwar ta cika makil a yanzu, kuma akwai fiye da kima cewa manyan kamfanoni da manyan 'yan kasuwar crypto a yanzu suna fitowa don siyan kadarori na kudaden intanet kamarsu bitcoin da ether.

Bujuman 'yan crypto tuna suka fara tara miliyoyin daloli na bitcoin tare da tunanin cewa zai iya zama ma'ajiyar darajar kudi a nan gaba kadan.

Yanzu dai bitcoin ya sauka kasa da kusan 40% cikin 100% daga darajarsa ta kololuwa ta dalar Amurka 68,000 a wannan shekara.

Bujuman 'yan crypto ne dai ke da makulin juya akalar farashi da dajarar bitcoin, wadanda ke iya motsa kasuwarsa yadda suka so.

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

'Yan crypto dai sun tafka asarar sama da Naira tiriliyan 20.14 a cikin sa’o’i 24 yayin da farashin bitcoin ya dungura zuwa kasa da dala 40 a karon farko tun daga watan Maris.

Bacin rana: Yadda ƴan crypto suka sharɓi hawayen asarar N20tr cikin sa'o'i 24

A wani labarin, 'yan crypto sun yi asarar sama da Naira Tiriliyan 20 a rana guda yayin da farashinsa ya fadi kasa da dala dubu 40 a karon farko tun ranar 16 ga Maris, lamarin da ya kai ga kassara kusan ‘yan kasuwa 150,000 a kasuwar.

Faduwar farashin bitcoin na zuwa ne a daidai lokacin da masu zuba jari ke auna hadarin hauhawar farashin ruwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma wargajewar kasuwannin duniya sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Farashin bitcoin ya fara ne a ranar Litinin, 11 ga Maris da jarin dalar Amurka biliyan 803 kafin rufewarsa a ranar da dalar Amurka biliyan 754.5 yayin da aka tafka asarar dala biliyan 48.4 cikin sa'o'i.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Zan Iya Sanadin Samar Da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Mace a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel