Bacin rana: Yadda ƴan crypto suka sharɓi hawayen asarar N20tr cikin sa'o'i 24

Bacin rana: Yadda ƴan crypto suka sharɓi hawayen asarar N20tr cikin sa'o'i 24

  • 'Yan crypto sun ga asarar sama da Naira tiriliyan 20 yayin da farashin kudaden intanet suka karye a kasuwar duniya cikin sa'o'i 24
  • Kimar kasuwa mafi shahara a kudin intanet ta ragu yayin da farashin bitcoin ya fado kasa da dala 40 wanda ya sa ya zama mafi sauka tun tsakiyar Maris
  • Bitcoin ba shine kawai kudin intanet da ke da mummunan rana ba kamar yadda Ethereum da sauran tsabobin intanet su ma suka ragu sosai

'Yan crypto sun yi asarar sama da Naira Tiriliyan 20 a rana guda yayin da farashinsa ya fadi kasa da dala dubu 40 a karon farko tun ranar 16 ga Maris, lamarin da ya kai ga kassara kusan ‘yan kasuwa 150,000 a kasuwar.

Faduwar farashin bitcoin na zuwa ne a daidai lokacin da masu zuba jari ke auna hadarin hauhawar farashin ruwa, hauhawar farashin kayayyaki da kuma wargajewar kasuwannin duniya sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

Kara karanta wannan

Ramadana: Yadda kankara ta zama kamar nama a Kano saboda tsananin zafi

Farashin bitcoin ya fara ne a ranar Litinin, 11 ga Maris da jarin dalar Amurka biliyan 803 kafin rufewarsa a ranar da dalar Amurka biliyan 754.5 yayin da aka tafka asarar dala biliyan 48.4 cikin sa'o'i.

Bacin rana ga 'yan crypto
Bacin rana: Yadda 'yan crypto suka sharbi hawayen asarar N20tr cikin sa'o'i 24 | Hoto: Bitcoin chart
Asali: Facebook

A lokacin rubuta wannan rahoton, farashin ya koma dala dubu 40.3 idan aka kwatanta da farashin dala dubu 39.34 da aka gani a ranar Litinin, 11 ga Afrilu 2022, bisa bayanan shafin diddigin kudaden intanet, Coindesk.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Coinglass kuma ya ba da rahoton cewa sama da dala miliyan 439 aka rasa a zagayen kasuwar crypto a cikin awanni 24.

Hakan ya hada da harkalloli 141,000, wanda daya daga cikinsu ya yi asarar dala miliyan 10 a cinikinsa.

Sauran kadarorin intanet da rage kima

A fadin kasuwannin crypto, kusan dala miliyan 152 ne suka narke a tsagin Bitcoin, sabanin dala miliyan 103 a fannin Ethereum.

Kara karanta wannan

Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi

Ethereum, mafi girma na biyu a kasuwar cryto, farashinsa ya sauka zuwa dala dubu uku, raguwar sama da 6% kenan tun tsakiyar watan da ya gabata, in ji Nairametrics.

Altcoins kuwa irin su Terra's LUNA token, SOL, da ADA suma sun sha fama mara dadi. Hakanan an ga asara tsabobin memes ko sh*t wato Dogecoin da Shiba Inu.

Gonar kudi: Yadda matashi ya sayar da hoton tsaleliyar budurwa N600k a duniyar crypto

A wani labarin, wani hazikin matashin madaukin hotuna a Najeriya, Adisa Olashile, ya yi amfani da karfin fasahar blockchain ta hada-hadar kudaden intanet wajen cika aljihunsa da kudi.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan da ya sayar da hotunan wani tsohon makadi a kafar NFT ta OpenSea kan kudi sama da miliyan daya. Sannan ya yi alkawarin bai wa tsohon 50% na abin da ya samu.

A cikin wani rubutu a ranar Laraba, 6 ga Afrilu, hazikin matashin ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa ya siyar da hoton wata budurwa a matsayin Non-Fungible Token (NFT) akan Foundation, wata kafar musayar NFT.

Kara karanta wannan

Inda ranka: Tashin hankali yayin da wani ya bude asusunsa ya ga takardu a madadin kudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel