Mai neman Shugaban kasa ya ce Najeriya za tayi takara da Amurka idan ya samu mulki

Mai neman Shugaban kasa ya ce Najeriya za tayi takara da Amurka idan ya samu mulki

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya ce a cikin shekaru hudu kacal zai iya rikidar da tattalin arzikin kasar nan
  • Orji Uzor Kalu ya yi alkawarin cewa karfin tattalin Najeriya zai zama kamar na Amurka da Jafan
  • ‘Dan takarar Shugaban kasar ba zai nemi tuta idan ba yankin shi APC ta kai takara a zaben 2023 ba

Abuja – Sanata Orji Uzor Kalu ya cika baki cewa karfin tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa a cikin shekaru hudu muddin ya zama shugaban kasa.

PM News ta rahoto shugaban masu tsawatarwa a majalisar dattawan ya na wannan alkawari a lokacin da ‘yan jarida suka yi hira da shi a garin Abuja.

A cewar Orji Uzor Kalu, karfn GDP na Najeriya zai zama tamkar na Amurka, Jafan da sauran manyan kasashen Duniya, idan ya karbi shugabanci.

Kara karanta wannan

Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce tsohon gwamnan na jihar Abia ya amsa tambayoyi ne a game da burin da yake da shi na karbar mulki a 2023.

Orji Kalu ya ce dole ne wanda zai zama shugaban kasa ya zama wanda zai iya bunkasa tattalin arzikin Najeriya, ya inganta tsaro, ya sa jama’a farin ciki.

Mutane 13, 000 Kalu ya ba aiki

Tsohon gwamnan ya bada misali da kan shi, ya ce akwai mutane 13, 000 da ke cikin abinci a karkashinsa a sanadiyyar ayyuka iri-iri da ya sama masu.

Sanatan APC
Sanatan Abia, Orji Uzor Kalu Hoto: @orji.kalu.79
Asali: Facebook
“Zan iya canza tattalin arzikin Najeriya a shekaru hudu, zan maida karfin jimillar tattalin arzikin mu ya rika takara da na Amurka, Jafan da sauransu.”
“Kowa yana cewa shi ‘dan takara ne, aikin me suka taba yi? Me suka yi wa jama’a? Sun iya kafa mutane? Ni na dauki mutane 13, 000 aiki a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

“Kuma ina da karfin da zan iya jagorantar mutane.” - Sanata Orji Uzor Kalu

Zan yi takara idan …

People Gazette ta rahoto ‘Dan majalisar yana cewa zai nemi takara ne da sharadin cewa mutumin kudu maso gabas aka yarda za a ba tikitin jam’iyyar APC.

Kalu ya ce Kudu maso gabas da Arewa maso gabas ne kurum ba su taba fitar da shugaban kasa ba, idan aka ba su dama a 2023, zai kai jam’iyyarsa ga nasara.

Tinubu ya yi taro a Legas

Bola Tinubu ya samu nasara a zaman da ya yi da shugaban majalisun dokoki na jihohi a garin Legas, ya samu kwarin gwiwar neman tikiti a jam'iyyar APC.

An ji cewa shugaban kungiyar ‘yan majalisar dokokin Najeriya, Rt. Hon. Abubakar Sulaiman ya yi wa Bola Tinubu alkawari su na tare da shi a takarar da zai yi.

Kara karanta wannan

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

Asali: Legit.ng

Online view pixel