Abuja: Saurayi, Ahmed, Ya Jagoranci Garkuwa Da Budurwarsa, Ya Karɓi Fansar N2m Daga Hannun Iyayenta
- Wani Ahmed yana hannun ‘yan sanda bayan an kama shi da laifin hada kai da wani Uchenna Daniels wurin yin garkuwa da budurwarsa, Hannatu Kabri
- An yi garkuwa da Kabri ne a Abuja, ranar 31 ga watan Maris inda aka zarce da ita Jihar Legas, kuma an sako ta ne bayan iyayenta sun tura N2m a matsayin kudin fansa
- Bayan kai wa ‘yan sanda rahoto ne suka fara bincike don gano wanda ya yi aika-aikar daga nan suka kamo Daniels wanda ya tona saurayinta kamar yadda Kakakin ‘yan sanda, SP Benjamin Hundeyin ya bayyana
Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta kama wani Ahmed bisa zarginsa da garkuwa da budurwarsa, Hannatu Kabri bayan hada kai da wani Uchenna Daniels, rahoton Daily Trust.
Daniels ya sace Kabri a Abuja a ranar 31 ga watan Maris sannan ya zarce da ita Legas.
News Wire NGR ta rahoto yadda ‘yan sanda suka dage wurin farautar masu laifin wanda har ya kai ga an kama Daniels.
Yayin tattaunawa da manema labarai a hedkwatar ‘yan sanda da ke Ikeja a Jihar Legas, Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya ce ‘yan sanda suna kokarin kama wani Ahmed da Bilya wadanda ake zargin suna da hannu a lamarin.
Saurayinta ne ya shirya aika-aikar
A cewarsa:
“A ranar 31 ga watan Maris din 2022 da misalin karfe 2 na rana, bayanan sirri sun nuna yadda wani Uchenna Daniels mai shekaru 30 ya yi garkuwa da wata Hannatu Kabri mai shekaru 22 a Abuja ya zarce da ita Legas.
“Jami’an rundunar sun bi sawun wanda ake zargin, Uchenna Daniels a Allen Avenue da ke Ikeja. Daniels ya shaida cewa wani saurayin budurwar, Ahmed ne ya shirya garkuwa da ita kuma ya amshi kudin fansa N2 a Kaduna a wurin iyayenta kafin suka sake ta.
“Ya kara da cewa sun yi amfani da bindigar wasa ne wurin tafka laifin. Ana ci gaba da bincike don gano sauran masu laifin.”
Kakakin ‘yan sanda ya ce ba wannan kadai bane rahoton da aka kai musu na irin laifin nan
Kakakin ya ce wannan ne daya daga cikin kamen da suka yi a ‘yan kwanaki kadan cikin wata daya don yaki da ta’addanci a cikin Jihar Legas.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas, Abiodun Alabi ya tabbatar wa mazauna Legas cewa zai bayar da isasshen tsaro da kulawa garesu da dukiyoyinsu.
Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi
Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe
A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.
Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.
Asali: Legit.ng