Jirgin ruwa ya jawo Budurwar da ke daf da aure da mutum 28 sun yi shahada a Ramadan

Jirgin ruwa ya jawo Budurwar da ke daf da aure da mutum 28 sun yi shahada a Ramadan

  • An samu karin bayanai a game da hadarin jirgin ruwan da ya kashe mutane 29 a kauyen Sokoto
  • Mai garin Gidan Magana, Malam Muhammadu Auwal ya rasa ‘ya ‘yansa da ‘yanuwa har takwas
  • Hadarin ya auku ne ga kananan yaran da ke kokarin nemowa iyayensu itace domin a dafa abinci

Sokoto - Mutane 29 aka tabbatar da mutuwarsu a yayin da kwale-kwale ya kife a rafin Shagari a daidai wani kauye da ake kira Gidan Magana a Sokoto.

Jaridar Daily Trust ta fitar da cikakken rahoto a game da wannan hadari da ya auku a Gidan Magana da ke karamar hukumar Shagari, a jihar Sokoto.

Mafi yawan wadanda suka hallaka a hadarin kananan yara ne masu shekara tara zuwa 17 a Duniya, su na kokarin zuwa kauyen gaba domin su yi itace.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

Da kimanin karfe 8:00 na safiyar ranar Laraba wannan kwale-kwale ya kife dauke da mutane 35. An iya yin nasarar ceto mutane shida daga cikin fasinjojin.

Mai garin Gidan Magana ya yi magana

Mai garin kauyen Gidan Magana, Malam Muhammadu Auwal ya shaidawa Daily Trust ‘ya ‘yansa biyar suka gamu da ajalinsu a wannan mummunan hadari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mata 23 da kuma maza shida aka rasa a hadarin kamar yadda Muhammadu Auwal ya yi wa jaridar bayani, ya na zubar da hawaye saboda wannan rashi.

Jirgin ruwa
Wani kwale-kwale a ruwa Hoto: unsplash.com
Asali: UGC

Yara su kan yi ita ce domin a ci abinci

Mai garin na Gidan Magana ya ce su na wahala wajen samun abin da za su dafa abinci, don haka su kan je kauyukan da ke kewaye da su domin yin itace.

A cewar Mai garin, an samu labarin hadari ne a lokacin da manya su ke barcin bayan sallar asuba. Ko da aka isa rafin, ruwan ya cinye yara da-dama.

Kara karanta wannan

Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna

“Hadarin ya auku ne jim kadan bayan kwale-kwalen ya fara tafiya. Sai jirgin ya kubucewa matukin saboda ruwa ya yi karfi, sai ya kife.”
“Ina barci wasu matasa su ka zo gida suka sanar da ni. Na tara jama’an gari har da direbobinmu, ko da muka je, yara da yawa sun mutu.”
“Na rasa ‘ya ‘ya biyar da wasu kannen mata na su biyu. Na kuma rasa wata ‘yaruwa ta da aka sa aurenta mako daya bayan bikin sallah.”

- Muhammadu Auwal

Mutane shida sun yi rai

Asma’u, Na’ima da Hadiza masu shekara 8 zuwa 10 su na cikin wadanda suka yi rai. Mutanen kauyen sun ceto wasunsu a gabar ruwa bayan sun iya yin iwo.

Rahoton ya ce gwamnatin jihar Sokoto ta yi ta'aziyya ga mutanen Shinkafi a kan abin da ya faru.

Malaman addini sun mutu a Kano

A jiya aka ji cewa wasu malaman addinin Musulunci masu yawon wa'azi sun rasa rayukansu a jihar Kano a sakamakon mumunan hadarin mota a kan hanya.

Kara karanta wannan

Masu fasa bututu sun taso Najeriya a gaba, ana asarar Naira Biliyan 600 a kowace rana

Malaman sun yi hadarin mota ne a hanyar komawarsu gida daga karamar hukumar Sumaila. Su ma dai wadannan Bayin Allah sun cika ne a cikin watan azumi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel