Dan majalisa a Filato: An kashe makusantana fiye da 50 a harin 'yan bindiga

Dan majalisa a Filato: An kashe makusantana fiye da 50 a harin 'yan bindiga

  • Yusuf Adamu Gagdi, dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Pankshin-Kanke-Kanam, ya nuna alhini a kan kisan rashin tausayi da yan bindiga suka yiwa al'ummarsa
  • Dan majalisar ya ce ya san sama da mutane 50 cikin wadanda aka kashe da suna domin suna huldar siyasa da shi
  • Ya kuma yi addu'a kan Allah ya basu hakuri da dangana, inda ya ce ko shakka babu an yi masu mummunar barna

Plateau - Dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Pankshin-Kanke-Kanam ta jihar Filato, Yusuf Adamu Gagdi, ya magantu kan farmakin da yan bindiga suka kaiwa al’ummar mazabarsa.

Gagdi ya bayyana cewa zuwa yanzu, an tantance mutane sama da dubu hudu da suka gudu suka bar gidajensu ta sanadiyar tashin hankalin da ya afku a ranar Lahadi.

Dan majalisa a Filato: An kashe makusantana fiye da 50 a harin 'yan bindiga
Dan majalisa ya ce an kashe makusantansa fiye da 50 a harin Filato
Asali: UGC

BBC Hausa ta kawo cewa Gagdi ya kuma ce kawo yanzu ya tabbatar da mutuwar mutane fiye da cas’in.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Har ila yau, dan majalisar ya bayyana cewa zuwa yanzu ya tabbatar da mutuwar mutane sama da guda 90 wanda yace ya yiwa sama da mutum 50 daga cikinsu farin sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A hirarsa da wakilin BBC Hausa, an jiyo Gagdi yana cewa:

“Wannan wuri, wurine da bamu taba sanin fada ba, bamu taba sanin yaki ba, mu kuma mutanenmu ba masu tsokana bane. Mutum 92 da aka kashe babu wanda bai sanni da suna ba. Na san mutum sama da 50 a cikinsu da suna.
"Zan iya kiran sunan mutum 50 a cikin wadanda aka kashe wanda tun ina dan majalisa na jiha muna hulda da su, suna taimaka mana wajen zabe, suna taimaka mana wajen zaman lafiya, suna taimaka mana wurin kira ga mutane su zauna lafiya da juna.
“Babu wanda abun nan ya shafe shi fiye dani tunda a cikin mutanen nan akwai mutum 19 da sune suka yi mun kodinetan zabe a 2015 lokacin ina neman zabe na jaha. A 2019 mutum 24 ne a cikin wadanda aka kashe wadanda sune kodinatona na mazabu a wannan yankin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun kutsa cikin Masallaci, Sun bindige Sarki har Lahira ana Sallar Isha'i

"Toh ka ga idan akwai wanda abun ya taba ba wanda danshi aka kashe ba ni da nake huldar siyasa da wadannan mutane da aka kashe, mafiya yawansu ni aka yiwa wannan abu. Ina addu’a Allah ya sanyaya zuciyarmu a kan wannan rashi da aka yi, amma mu an yi mana barna.”

Legit.ng Hausa ta samu damar tattaunawa da wani dan asalin yankin Ali Mahe, wanda ke zaune a jihar Gombe, wanda ya shaida cewa, yana da kanensa da har yanzu bai samu a waya ba, kuma yana tsoron komawa garin.

Ya ce:

"Na kira kani na ba adadi bai dauka ba a farko, daga baya wayarsa switch off (a kashe). Na kira abokina wayar ba ta shiga kuma wallahi ina tsoron komawa. Na dai ji iyayena sun gudu.
"Na dawo nan ne a lokacin Korona, dama sana'ata gyaran mota ne, kuma shi nake anan. Nakan je gida lokaci zuwa lokaci, amma yanzu bansan ta ina zan fara ba."

Kara karanta wannan

Bayan harin Filato, yan bindiga sun sake kashe mutum 19 a wata jihar arewa

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

A gefe guda, mun kawo cewa an yi jana’izar mutanen da yan bindiga suka kashe a harin safiyar Lahadi da suka kai kauyuka hudu na jihar Filato.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa masoya da abokan arziki ne suka binne mamatan gaba daya a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu.

Mazauna yankunan sun bayyana cewa an samo sama da gawarwaki 100 kuma an binne su amma kuma babu wani adadi da rundunar yan sanda ko gwamnatin jihar ta fitar a hukumance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel