Innalillahi: Jirgin Ruwa Ya Kife a Sokoto, Mutum 28 Sun Mutu

Innalillahi: Jirgin Ruwa Ya Kife a Sokoto, Mutum 28 Sun Mutu

  • Kimanin mutane 26 na suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a Kogin Shagari da ke karamar hukumar Shagari a Jihar Sokoto
  • Shugaban karamar hukumar Shagari, Aliyu Dantani ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba a garin Sokoto
  • A cewarsa, lamarin ya auku ne a ranar Talata da yamma kuma cikin gawawwakin akwai mata 21 da yara 5, yanzu haka ana ci gaba da bincike ko za a gano wasu

Jihar Sokoto - Wani jirgin ruwa ya kife a Kogin Shagari da ke karamar hukumar Shagari a Jihar Sokoto wanda hatsarin ya janyo asarar rayuka 26, Channels TV ta ruwaito.

Innalillahi: Jirgin Ruwa Ya Kife a Sokoto, Mutum 28 Sun Mutu
Jirgin Ruwa Ya Kife a Sokoto, Mutum 28 Sun Mutu. Hoto: Daily Nigerian.

Aliyu Dantani, shugaban karamar hukumar Shagari ne ya shaida wa wakilin NAN a ranar Laraba a Sokoto inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Talata da yamma.

Kara karanta wannan

Har Da Kano: Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana ci gaba da bincike

Daily Nigerian ta rahoto cewa Dantani ya ce an gano gawawwaki 26, wadanda cikinsu akwai mata 21 da yara 5, kuma yanzu haka ana ci gaba da bincike don gano ko akwai wasu.

Dantani ya ci gaba da cewa ba a san yawan fasinjojin da suka shiga cikin jirgin ruwan ba.

A cewarsa yanzu haka direbobin jirgin ruwan suna cikin kogin suna ci gaba da bincike don gano gawawwaki ko kuma tsaratar da masu rai.

Hatsarin jirgin ruwa ya halaka magidanci, matansa biyu da dansa a Neja

A wani rahoton, kun ji cewa A kalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a kauyen Zhigiri a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai wani magidanci mai suna Mallam Mu'azu Babangida, matansa biyu da kuma babban dansa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

Kakakin gamayyar kungiyar Shiroro, Salis Mohamed Sabo, ya fada ma jaridar cewa lamarin ya afku ne lokacin da mazauna kauyen suke hanyarsu ta zuwa Dnaweto, wani kauye da ke makwabtaka domin halartan taron suna da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164