Har Da Kano: Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku

Har Da Kano: Buhari Ya Amince a Buɗe Sabbin Polytechnic a Wasu Jihohi Uku

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bude wasu sabbin Polytechnic guda uku a cikin wasu jihohi don saukaka wa mutane samun karatun gaba da sakandare
  • Darektan watsa labarai da hulda da jama’an Ma’aikatar Ilimi, Mr Ben Bem Goong ya bayyana hakan ta wata takarda da ya saki a Abuja
  • A takardar ta ranar Talata ya ce Polytechnic din guda uku sun hada da na Umunnoechi a Jihar Abia, Orogun a Jihar Delta da kuma Kabo a Jihar Kano

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bude Kwalejojin Fasaha (Polytechnic) guda uku na tarayya a bangarori daban-daban na kasar nan a matsayin hanyar saukaka wa jama’a damar samun ilimin gaba da sakandare.

A wata takarda wacce Darektan watsa labarai da hulda da jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta tarayya, Mr Ben Bem Goong ya saki a ranar Talata a Abuja ya shaida hakan.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da Janar din Sojan Bogi kan damfarar miliyoyi

Buhari Ya Amince Da buɗe Sabbin Polytechnic Guda 3 A Jihar Kano Da Wasu jihohi
Buhari Ya Amince Da buɗe Sabbin Polytechnic Guda 3 A Wasu jihohin Najeriya. Hoto: Nigerian Tribune.
Asali: Twitter

A cewarsa Polytechnic din guda uku sun hada da na Umunnoechi da ke Jihar Abia, Orogun da ke Jihar Delta da Kabo a Jihar Kano, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Mashawarcin shugaban kasa a bangaren kafafen watsa labarai na zamani, Bashir Ahmad shima ya tabbatar da rahoton kafa kwalejojin uku a shafinsa na Twitter.

Za su fara aiki a watan Oktoba mai zuwa

Nigerian Tribune ta nuna inda ya ce sabbin kwalejin na Fasaha din za su fara aiki ne a watan Oktoban 2022.

Idan aka tattara, yanzu haka akwai Foliteknik guda 36 na tarayya da ke cikin Najeriya.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel