Farmakin Filato: An samo sama da gawawwaki 50, an babbake gidaje 100

Farmakin Filato: An samo sama da gawawwaki 50, an babbake gidaje 100

  • A kalla gawawwaki 50 aka samu inda wasu gidaje 100 suka babbake sakamako farmakin 'yan ta'adda a kauyukan Plateau
  • kamar yadda mazaunin kauyen Kukawa ya sanar, an samu gawawwaki 24 aka samu a Kukawa, 15 a Gyanbahu, 8 a Dungur sai 4 a Keram
  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma yace an aike jami'an tsaro yankunan

Plateau - An samu sama da gawawwaki 50 a kauyukan karamar hukumar Kanam ta jihar Filato kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kutsa kauyukan a ranar Lahadi.

Farmakin Filato: An samo sama da gawawwaki 50, an babbake gidaje 100
Farmakin Filato: An samo sama da gawawwaki 50, an babbake gidaje 100. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

'Yan bindigan sun kai samame kauyukan Gyanbahu, Dungur da Keram inda suka halaka mutane masu yawa tare da kone sama da gidaje 100 kamar yadda ganau suka tabbatar.

Kara karanta wannan

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

A yayin tsokaci km farmakin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya ce, "Hukumar 'yan sandan ta san da farmakin; an tura 'yan sanda yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Har a halin yanzu ban samu bayani kan yawan wadanda aka kashe da gidajen da aka kone. Zan sanar da ku halin da ake ciki idan na samu."

Sai dai, Adam Musa, mazaunin Kukawa, daya daga cikin kauyukan da lamarin ya shafa ya sanar da Daily Trust cewa gawawwaki 24 aka samu a Kukawa, 15 a Gyanbahu, 8 a Dungur sai 4 a Keram.

Ya kara da cewa, an tura wadanda suka samu raunika asibitoci daban-daban har da babban asibitin Dangi da ke karamar hukumar Kanam ta jihar.

Musa ya kara da cewa idan an samu dukkan gawawwakin, za a yi musu jana'iza tare da birne su.

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Ya ce tuni aka aika jami'an tsaro yankunan da tarzomar ta shafa.

A halin yanzu, manyan hanyoyin Jos, babban birnin jihar da kuma hanyoyin ofisoshin hukumomin tsaro duk an toshe su da jami'an tsaro a ranar Lahadi sakamakon rade-radin da ake yi kan cewa za a kai farmaki wuraren, Daily Post ta ruwaito.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai mugun farmaki sansanin soji, sun sheke dakaru 11

A wani labari na daban, a kalla sojoji 11 ne aka kashe a mugun hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wani sansanin soji da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda majiya ta shaida wa TheCable.

‘Yan bindigar da suka isa sansanin da yawansu sun kutsa cikin sansanin da ke kauyen Polwire a ranar Litinin da ta gabata inda suka yi artabu da sojojin.

Majiyar soji ta shaida wa jaridar TheCable cewa, ‘yan bindigar sun bayyana a kan babura kuma suna dauke da manyan makamai da suka hada da gurneti (RPG).

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Asali: Legit.ng

Online view pixel