Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi

Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi

Sakamakon umurnin gwamnatin tarayya, an toshe layuka milyan 72.77 daga kiran waya sai sun hada layukansu.

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin, 14 ga Afrilu, ta umurci kamfanin sadarwa su hana kira fita daga duk wani layin da ba'a hada ba.

Amma wasu yan Najeriya sunce duk da sun hada layukansu da NIN, an toshesu daga kiran waya.

A cewar BBC News Pidgin, wani babban jami'in daya daga cikin kamfanonin sadarwa ya lissafo dalilan da ka iya haifar da hakan.

Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi
Shin ka hada layin wayarka da NIN amma har yanzu ba ka iya kira? Ga abinda zaka yi Hoto: @WithinNigeria, @thecableng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa sune:

  • Idan mutum bai kammala rijista ba
  • Kuskuren na'ura
  • Hada NIN da layuka da yawa
  • Matsalar yanar gizo
  • Kuskure yin abinda ya kamata daga NIMC

Abinda za kayi idan layinka na toshe duk da ka hada da lambar NIN

Kara karanta wannan

Layin dogon jirgin kasa: Ku godewa Buhari, Amaechi ga Yan Najeriya

Jami'in ya kara da cewa duk wanda hakan ya shafa ya garzaya ofishin kamfanin sadarwarsa ka gabatar da korafi.

Ya ce kamfanonin sadarwa ba su jin dadin toshe layukan da ake yi saboda asarar kudin shiga sukeyi, saboda haka zasuyi gaggawan ganin an magance matsalar.

Rahoton ya kara da cewa shugaban hukumar NIMC na Kano ya tabbatar da abinda jami'in ya fada.

Ya shawarci duk wanda hakan ya shafa su je ofishin kamfanin da suke amfani suyi korafi.

A cewarsa, kamfanonin zasu rubuta musu wasika su kaiwa NIMC, inda nan za'a duba takamammen matsalar kuma a gyara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng