Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna

Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna

  • Ana ci gaba da samun karin haske game da mutanen da ke tsare a hannun yan bindigar da suka farmaki jirgin kasa a Kaduna
  • A yanzu haka, an ce mutane 68 ne ke hannun maharan wadanda suka hada da mata 41, maza 22 da kananan yara biyar
  • An samu wannan bayani ne daga wajen tsohon manajan darakta na bankin noma, Alwan Hassan, wanda aka saki a makon da ya gabata

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 68 ne a hannun yan bindigar da suka sace matafiya daga wajen harin jirgin kasa na ranar 28 ga watan Maris.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, adadin wadanda ke tsare a hannun maharan ya hada da mata 41, maza 22 da kuma kananan yara biyar.

Da farko dai mun ji yadda yan bindiga suka dana bam a layin dogo, lamarin da ya tilasatawa jirgin tsaya inda su kuma suka bude wuta a kan fasinjoji.

Kara karanta wannan

Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci

Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna
Ya bayyana: Adadin Mata, Maza da Yaran da yan bindigan suka sace a harin jirgin Abuja-Kaduna Hoto: Humanglemedia.com
Asali: UGC

Kafin isowar jami’an tsaro, an kashe wasu daga cikin fasinjojin jirgin sannan aka yi garkuwa da wasun su.

Da take yin karin bayani kan lamarin bayan mako daya da faruwar lamarin, hukumar kula da ayyukan jiragen kasan Najeriya (NRC) ta ce bata san inda fashinjoji 146 suke ba.

Amma manajan darakta na bankin noma (BOA), Mista Alwan Hassan, wanda maharan suka saki a ranar Laraba da ya gabata ya bayyana adadin mutanen da ke tsare yayin da yake bayanin halin da ya shiga, rahoton Daily Trust.

Hassan, ya yi karin bayani kan wadanda aka sace da kuma halin da ya shiga a hannun masu garkuwa da mutanen a zantawa mabanbanta da ya yi da yan uwa, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da yan uwa sauran mutanen da aka sace.

Kara karanta wannan

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

Wani dan uwan daya daga cikin mutanen da aka sace ya ce shugaban na BOA ya fada masu cewa an sa mutanen yin tafiya na tsawon kwanaki biyar.

Ya ce akan bari su huta a sansanonin kan hanya kafin suka isa ainahin sansanin maharan da ke kusa da karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

An tattaro cewa ya gane wadanda aka sace da dama da sunansu da taimakon hotunan da yan uwansu suka gabatar masa.

Sai dai ya ce da yawa daga cikinsu su ji rauni ta sanadiyar harbin bindiga.

Hassan ya baiwa yan uwan mutanen da suka ziyarce shi tabbacin cewa dukka mutanen da ke tsare suna cikin koshin lafiya domin likitocin da maharan suka kawo suna kula da wadanda suka ji rauni.

Harin jirgin Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki sabon bidiyon fasinjoji, suna rokon gwamnati

A baya mun ji cewa wasu jerin bidiyoyi da jaridar HumAngle ta samu na farmakin da 'yan ta'adda suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga watan Maris ya bayyana miyagun dauke da muggan makamai a cikin kungurmin daji zagaye da wadanda suka sace inda jama'ar ke rokon gwamnati da ta dauka matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

A daya daga cikin bidiyoyin da suka saki kwanan nan wanda ya bambanta da wanda suka saki makon da ya gabata, an ga a kalla 'yan ta'adda 15 jere a bayan wadanda aka sacen rike da bindigogi inda suka rufe fuskokinsa da rawuna.

Bayyana bidiyoyin ya nuna babu ko shakka 'yan ta'adda na cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yamma makamancin yadda 'yan ta'addan yankin tafkin Chadi ke yi. Farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna babu shakka 'yan ta'adda ne suka kai shi ba 'yan bindiga ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel