Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

  • Rahoto daga jihar Osun na bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun bi dare sun hallaka shugaban jam'iyyar APC na karamar hukuma
  • Wannan lamari ya faru ne a daren jiya, inda suka bi shi har cikin dakinsa suka bindige shi har lahira
  • Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta tabbatar da faruwan lamarin, kana ta bayyana matakin da take dauka a yanzu

Wasu ‘yan bindiga a safiyar yau Litinin sun kashe shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Atakumosa East Central a jihar Osun, Cif Gbenga Ogbara.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, an harbe Ogbara ne a cikin dakinsa da ke Igangan, garinsu da misalin karfe 12 na dare.

'Yan bindiga sun bindige shugaban APC a Osun
Yanzu-Yanzu: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Wata majiya ta nuna cewa an ajiye gawar Ogbara a asibitin Wesley Guild, Ilesa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

A halin da ake ciki, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Mrs Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Opalola ta ce:

“Wasu ‘yan bindiga ne suka kashe shugaban APC da misalin karfe 12 na dare. Tuni dai aka tura ‘yan sanda yankin. Ana ci gaba da bincike kan lamarin. Masu laifin ba za su tsere wa shari’a ba.”

Rahoton gidan talabijin na Channels ya ce an ajiye gawar marigayin a asibitin Wesley Guild da ke Ilesa.

Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Joseph Makoju, ya rigamu gidan gaskiya

A wani labarin, jaridar Leadership ta rahoto cewa Injiniya Joseph Oyeyani Makoju, tsohon Manajan Datakta na kamfanin Simintin Ɗangote, ya rasu ranar 11 ga watan Afrilu, 2022.

Duk da babu cikakken bayani kan musabbabin da ya jawo mutuwarsa, rahoto ya nuna cewa Makoju, ya rasu ne a wani Asibitin kudi a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje

Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da cewa Marigayin ya mutu ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.