Da Duminsa: Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Joseph Makoju, ya rigamu gidan gaskiya

Da Duminsa: Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Joseph Makoju, ya rigamu gidan gaskiya

  • Tsohon hadimin shugabannin Najeriya, Injiniya Makoju, ya riga mu gidan gaskiya a wani Asibitin kudi a Abuja
  • Makoju, wanda bai jima da aje aiki daga matsayin Manajan Darakta na kamfanin Simintin Ɗangote ba, ya rasu yau Litinin
  • Babu wani cikakken bayani kan ciwan da ya yi sanadin mutuwar babban mutumin a Najeriya

Abuja - Jaridar Leadership ta rahoto cewa Injiniya Joseph Oyeyani Makoju, tsohon Manajan Datakta na kamfanin Simintin Ɗangote, ya rasu ranar 11 ga watan Afrilu, 2022.

Duk da babu cikakken bayani kan musabbabin da ya jawo mutuwarsa, rahoto ya nuna cewa Makoju, ya rasu ne a wani Asibitin kudi a babban birnin tarayya Abuja.

Tsohon shugaban kamfanin simintin Ɗangote, Joseph Makoju.
Da Duminsa: Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Joseph Makoju, ya rigamu gidan gaskiya Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da cewa Marigayin ya mutu ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar rana.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Wasu ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun

Makoja ya yi aiki a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin wutar lantarki ga tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan da kuma Olesegun Obasanjo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan, ya jagoranci ƙungiyar masu samar da Siminti ta Najeriya da kuma wata hukumar wuta ta nahiyar Afirka mai suna, West African Power Pool Executive Board.'

Marigayin bai jima da yin ritaya daga matsayin Manajan Darakta/CEO na kamfanin Simintin Ɗangote, muƙamin da rike tun daga shekarar 2018, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

A wani labarin kuma Bola Tinubu ya maida martani kan ayyana takarar mataimakin shugaban ƙasa

Tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, da ɗansa bane.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da gwamnonin APC, Tinubu yace ɗan sa be girma haka ba.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya bai wa wadanda masallaci ya murkushe kyautar N5m a Yobe

Asali: Legit.ng

Online view pixel