Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

  • Sansanin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na siyasa, an ce ya fara neman zabi idan APC ta gagara gabanin zaben shugaban kasa na 2023
  • An ce wasu abokan tsohon gwamnan na jihar Legas sun firgita saboda shirun da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi game da burin Tinubu
  • Game da shirun shugaban kasan, rahotanni na cewa hakan na tada hankula a sansanin masu yakin neman takarar Tinubu gabanin zaben fidda gwanin da aka shirya yi a watan Yunin 2022

FCT, Abuja – Wani rahoto da jaridar BusinessDay ta buga na nuni da cewa, Bola Tinubu, jigo a jam’iyyar APC, ya fara tuntubar jam’iyyar SDP, a matsayin wata hanyar da zai bi wajen tabbatar da aniyarsa ta gaje Buhari, idan APC ta kasa ba shi tikitin takara.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

A cewar rahoton, majiyoyi na kusa da SDP sun ce Tinubu ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar a kwanan baya domin neman ma kansa masaukin siyasa.

Yiwuwar komawar Tinubu SDP
Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya | Hoto: punchng.com

Matakin da Tinubu ya dauka, an ce ya samo asali ne sakamakon lamarin da ya kai ga fitar da ‘yan takarar shugabancin jam’iyyar APC da wasu mukamai a babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja.

Wani jigo a jam’iyyar APC a cikin rahoton ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tinubu ba zai bar komai haka kawai ba yayin da ake ci gaba da rububin siyasa a tsakanin manyan ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.
“Shugabanmu ba zai yi jigilar tallafa wa wani bare ba. Ya jajirce sosai wajen ganin Najeriya ta kasance a halin da take yanzu kuma zai zama butulci ga Najeriya, ga duk wanda ya hana Tinubu karbar tikitin takarar shugaban kasa a 2023.”

Kara karanta wannan

Takarar shugabancin Tinubu ya samu gagarumin goyon baya daga wata kungiyar arewa

Shi ma wani jigo a jam’iyyar SDP ya tabbatar da labarin yana mai cewa:

“Tinubu ya tunkari jam’iyyar. Muna tattaunawa da shi, kuma zuwansa jam’iyyar zai taimaka mana wajen karfafa jam’iyyar.”

Tunde Rahman, mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yada labarai, ya musanta hakan yana mai cewa:

"Tinubu bai yi tunani ba kuma baya tunanin komawa wata jam'iyyar siyasa. Babu ko kadan; ba SDP da ka ambata ba, kuma ba wata jam’iyyar siyasa ba. Ba shi da bukata.
“Ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC. Kuma yana mai da hankali kan hakan.
“A halin yanzu Tinubu yana ratsa ko’ina cikin kasar nan, yana hada kai da masu ruwa da tsaki da kuma tallata takararsa. Abin da na sani ke nan.”

Bidiyon Sanata Abdullahi Adamu yayin da ya isa fadar shugaban kasa domin ganawa da Buhari

A yanzu haka, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga cikin wata ganawar sirri da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar

Wannan shine karo na farko da Sanata Adamu ke ganawa da shugaban kasar tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban jam’iyyar mai mulki na kasa a yan makonni da suka gabata.

Mai ba shugaban kasa shawara a shafukan sadarwa ta zamani, Bashir Ahmad ne ya sanar da batun ganawar tasu a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter.

Sanata Adamu ya samu rakiyar Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe zuwa ganin shugaban kasar a fadar gwamnati da ke babbar birnin tarayya, Abuja.

Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa

A gefe guda, mun kawo a baya cewa sabon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi jagorancin jam'iyya ta ƙasa daga hannun shugaban riko.

Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya babban taro kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya damƙa ragamar APC a hannun Adamu a hukumance.

Kara karanta wannan

APC ta shiga cikin hargitsi da Sanata Adamu su ka zama shugabannin jam’iyya na kasa

Hakan ya kawo ƙarshen tsawon watanni 21 da Buni ya jagoranci APC tun bayan naɗa shi shugaban kwamitin riko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel