Harin jirgin Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki sabon bidiyon fasinjoji, suna rokon gwamnati

Harin jirgin Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki sabon bidiyon fasinjoji, suna rokon gwamnati

  • 'Yan ta'addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sake sakin sabon bidiyon fasinjojin da suka yi garkuwa da su
  • A bidiyon, an ga daya daga cikin fasinjojin na bayyana cewa akwai iyaye mata, yara, tsoffi, marasa lafiya da kuma jigatattu a cikinsu, don haka gwamnati ta cika sharudda
  • Duk da har yanzu ba a san sharuddan da 'yan ta'addan suka gindaya wa gwamnati ba, a bayyane yake cewa mambobin kungiyar ta'addanci ne suka kai farmakin

Kaduna - Wasu jerin bidiyoyi da jaridar HumAngle ta samu na farmakin da 'yan ta'adda suka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na ranar 28 ga watan Maris ya bayyana miyagun dauke da muggan makamai a cikin kungurmin daji zagaye da wadanda suka sace inda jama'ar ke rokon gwamnati da ta dauka matakin gaggawa.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

A daya daga cikin bidiyoyin da suka saki kwanan nan wanda ya bambanta da wanda suka saki makon da ya gabata, an ga a kalla 'yan ta'adda 15 jere a bayan wadanda aka sacen rike da bindigogi inda suka rufe fuskokinsa da rawuna.

Harin jirgin Abuja-Kaduna: 'Yan ta'adda sun saki sabon bidiyon fasinjoji, suna rokon gwamnati
Wasu daga cikin fasinjojin da 'yan ta'adda suka sace a farmakin jirgin kasa na Abuja- Kaduna. Hoto daga Humanglemedia.com
Asali: UGC

Bayyana bidiyoyin ya nuna babu ko shakka 'yan ta'adda na cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yamma makamancin yadda 'yan ta'addan yankin tafkin Chadi ke yi. Farmakin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna babu shakka 'yan ta'adda ne suka kai shi ba 'yan bindiga ba.

HumAngle ta gano cewa, 'yan ta'adda sun mika wa gwamnati bukatarsu domin su saki wadanda suka sace amma har yanzu gwamnatin bata dauka mataki ba. Har a halin yanzu HumAngle bata tantance mene ne bukatun ba duk da an gano daya daga ciki shine sakin wasu daga cikin 'yan kungiyar da ke tsare.

Kara karanta wannan

Wadanda suka kai hari jirgin Abuja-Kaduna sun saki bidiyo, sun ce ba kudi suke bukata ba

Alamu na nuna cewa an dauka wannan sabon bidiyon ne tare da tsohon ganin cewa manajan daraktan Bankin Manoma, Alwan Ali-Hassan wanda ya bayyana a tsohon bidiyon ya sake bayyana a sabon amma ya kubuta bayan biyan zunzurutun kudi.

"Mu ne fasinjojin da suka bar Abuja zuwa Kaduna a ranar 27 ga watan Maris din 2022," daya daga cikin jama'ar yace.
"A kan hanyarmu aka kai mana farmaki kuma aka yi garkuwa da mu. Daga wannan lokacin zuwa yanzu, mu kadai ne muka san irin halin da muke ciki. Akwai iyaye mata a cikinmu, akwai yaran goye. Akwai tsofaffi da marasa lafiya. Da yawanmu ba mu da lafiya. Muna cikin mawuyacin hali. Muna kira ga 'yan uwa, abokanmu da gwamnati da su dauka matakin gaggawa."

A yayin da mutumin ke magana, Alwan Hassan na hannunshi na dama yayin da wani ke na hagu. Sai kamara ta matsa inda ta haska 'yan ta'addan wasu na zaune yayin da wasu ke kishingide.

Kara karanta wannan

Diraktan bankin BOA da aka sace a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya samu yanci

Bayan nan, an ga Ali-Hassan yana kara kira ga gwamnati da ta saurari wadanda aka sace tare da cika sharuddan da wadanda suka sace su suka gindaya.

A bidiyon na biyu, an ga mata hudu a jere, wata daliba wacce tace sunanta Lois John tana karantar fannin noma da kiwo a jami'ar jihar Kaduna kuma tayi magana a madadin matan.

Daya daga cikin matan mai matsakaicin shekaru ta bayyana sunanta da Gladys, tsohuwar ma'aikaciyar masana'antar tsaro ce ta Kaduna.

"Abinda ya faru a ranar Litinin bai dace ya faru ba," tace. Ta yi kira ga gwamnati da ta saurari wadanda suka sace su.

A yayin da bidiyon baya ya nuna 'yan ta'addan na magana, sabbin bidiyoyin biyu sun nuna wadanda aka sace suna rokon gwamnati ne.

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Kara karanta wannan

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

A wani labari na daban, hukumar kula da ayyukan jirgin kasan Kaduna sun yi karin haske kan gazawar jami’ai a matakai daban-daban wajen dakile farmakin da aka kai wa jirgin kasa, wanda aka samu gargadi tun watanni da suka gabata.

Wasikun da aka aike wa hukumomin tsaro da Daily Trust ta gani sun bayyana yadda aka bankado wannan makarkashiyar biyo bayan kutsen da jami’an leken asiri suka yi wanda ya kai ga fitar da sanarwar ga hukumomi daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel