Yahaya Bello: Zan Iya Sanadin Samar Da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Mace a 2023
- Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce zai zabi mace a matsayin mataimakiyarsa idan har aka tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC na zaben 2023
- Ya bayyana hakan ne a taron GYB na biyu na shekarar nan wanda aka shirya don harkar siyasa da masu hadin kai wurin aikata laifuka, wanda aka yi Abuja, inda ya ce zai bai wa mace damar tsayawa tare da shi
- A cewarsa ya daura dammarar yin aiki da matasa, mata da masu nakasa kamar yadda ya yi a Kogi kuma ba zai bar kowa a baya ba don yanzu haka yana shirin mayar da mutane miliyan 100 miloniyoyi
Abuja - Yahaya Bello, gwamnan Jihar Kogi ya ce zai tsayar da mace a karon farko ta zama mataimakiyarsa in har aka tsayar da shi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a gagarumin zaben 2023 da ke karatowa, rahoton NAN.
Bello ya bayar da wannan tabbacin ne a taron GYB na biyu na shekara wanda aka shirya don harkar siyasar Najeriya da masu hada kai wurin laifuka wanda aka yi a Abuja inda ya ce matsawar aka ba shi dama zai dama tare da mata.
Gwamnan ya ce ya zage damtse wurin yi aiki tare da mata, matasa da masu nakasa kamar yadda ya yi a Jihar Kogi kuma zai tabbatar bai bar kowa a baya ba.
Ya ce idan aka ba shi dama zai fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci
A cewarsa:
“Idan aka ba ni dama, in jam’iyyata ta tsayar da ni kuma ta ba ni damar zaben wanda zamu tsaya tare da shi, ba zan tafi ba sai da uwata, wacce mace ce.
“Ina mai tabbatar muku, da za a bani dama da ni zan samar da mataimakiyar shugaban kasa mace ta farko a 2023.”
Daily Nigerian ta nuna yadda Bello ya ce idan ya samu dama, mulkinsa zai mayar da hankali wurin tallafa wa jama’a don tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa.
A cewarsa, a mukinsa matsayin gwamnan Jihar Kogi, ya bunkasa miloniyoyi 2,000, inda ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci.
Bello ya ce za su tabbatar babu bambancin addini, yare ko yanki
A cewarsa, tarin nasarorin da ya samu ne ya sanya har ya tsaya takara duk da matakan da jam’iyyar ta samar wurin tsayar da dan takara.
A cewarsa, jam’iyyarsa ce za ta samar da shugaban kasa mai zuwa saboda APC tana da dabaru. Kuma jam’iyyar za ta tsayar da matashi wanda zai maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bello ya ci gaba da cewa mulkinsu zai tabbatar da cewa babu bambanci tsakanin mabiya addinai, yare da kuma yankuna na daban-daban.
'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa
A bangare guda, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.
PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.
Asali: Legit.ng