Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

  • Dan takarar jam'iyyar APC ya tado da batu mai muhimmanci, inda yace sam ba a son matasa su shiga siyasa
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan tsadar kudin sayen fom din tsayawa takara a zabe mai zuwa
  • Ya bayyana cewa, tsadar za ta hana matasa da dama damar nuna gogewarsu a fannin siyasa tunda basu da kudi

Wani dan takarar dan majalisa jam’iyyar APC, Christopher Ojo, ya yi Allah-wadai da tsadar kudaden sayen fom din takara a gabanin zaben 2023, inji rahoton Vanguard.

Ya yi tsokaci da cewa, matakin jam’iyyun siyasa shi ne ci gaba da tura masu arziki zuwa manyan kujerun siyasar kasar nan, wanda hakan ya saba da gangamin "Not Too Young To Run Act."

Ya yi nuni da cewa, matasa da dama da suke zaune cikin shiri su shiga a dama dasu a zabe mai zuwa sun karaya da wannan lamari na tsada.

Kara karanta wannan

Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

Shirin hana matasa takara a kasar nan
Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Ba a son matasa su yi mulki a Najeriya

Ya ce:

“Idan ba a fakaice ake ce mana mu jira wani lokaci ba ko watakila, mu shiga cikin ayyukan cin hanci da rashawa, a ina ne suke sa ran mu (matasa) za mu samu wannan makudan kudaden da za mu saya fom kawai.
“Daga abin da na gani ya zuwa yanzu, babu wata jam’iyya da ke sayar da fom kasa da Naira miliyan 3, an mance za a kashe makudan kudade wajen yakin neman zabe da sauran kayan aiki.
"Ku gaya mani, mu nawa ne za mu iya biyan wannan tsadar kudi amma duk da haka, suna mana da'awa game da damawa da kowa."

Ojo ya yi kira ga jam’iyyun siyasar da suka rigaya suka kayyade farashin fom din da su sake duba lamarin ta hanyar rage kudin

Kara karanta wannan

Najeriya na cikin wani hali: Tinubu ya ba wadanda harin 'yan bindiga na jirgin kasa ya shafa tallafin N50m

Inda ya kara da cewa:

“Idan shirin damawa da kowa gaskiya ne kuma muna son mu tabbatar da gaskiyar maganar gangamin ‘Not Too Young To Run Act’, to jam'iyyun siyasa dole ne cikin gaggawa su ga bukatar magance wannan matsala.”

Kafin tsokacin dan APC, tuni jam'iyyar LP ta bakin Comrade Abayomi Arabambi ya yi irin wannna batu kan tsadar kudin fom din takara, kamar yadda BluePrint ta tattaro.

Khadijat yar shekara 38 dake mafarkin gaje Buhari a 2023 ta shiga jam'iyya, ta faɗi wasu kalamai

A wani labarin, 'yar takarar shugabancin Najeriya, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana cewa ta rungumi jam'iyyar SDP ne saboda ita ce ta matasa da kuma mata.

Khadihat ta yi wannan jawabin ne ranar Alhamis yayin da take sanar da matakin komawa jam'iyyar SDP, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Da take jawabi, yar takarar wacce ba ta wuce shekara 38 ba a duniya, ta ce ta rungumi SDP ne saboda ta yi dai-dai da kudirinta da manufarta.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Asali: Legit.ng

Online view pixel