Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus

Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus

  • Tsohon shugaban soji na daya daga cikin jihohin arewa ya ce rashin shugabanci na kwarai ne a ko wanne mataki ya ke janyo hauhawar rashin tsaron kasar nan musamman a arewa
  • A cewarsa, idan aka samu shugabanci na kwarai kuma aka tanadar da makamai masu kyau ga sojojin Najeriya, cikin watanni 6 za a kawo karshen ‘yan ta’adda
  • Kamar yadda ya shaida, ya san yanzu haka ‘yan Najeriya sun fahimci babban kuskuren da suka tafka na zaben Buhari, kuma sun gane cewa ba zai iya tabuka komai ga kasar nan ba a matsayin shugaba

Tsohon shugaban sojin Najeriya na daya daga cikin jihohin arewa ya ce babban abinda ya ke janyo hauhawar rashin tsaro musamman a yankin arewa shi ne rashin jagorori na kwarai, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

ASUU ga FG: Ba zai yiwu ku yaki rashin tsaro ba yayin da kuka mayar dalibai 'yan zaman kashe wando

Kamar yadda ya shaida, idan aka samar da makamai masu kyau ga sojojin Najeriya, cikin watanni 6 za a gama da ‘yan ta’adda.

Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Watanni 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus
Za a Iya Kawo Karshen 'Yan Ta'adda Cikin Wata 6, Shugabannin Tsaro Masu Murabus. Hoto: The Punch
Asali: Depositphotos

A cewarsa:

“Zuwa yanzu, na yarda da cewa ‘yan Najeriya sun fahimci cewa sun yi babban kuskure na zaben Buhari kuma sun gane cewa ba zai iya wani shugabancin a zo a gani ba a kasar nan.”

Ya ce alawadai da fadar shugabanci ta ke yi ba mafita bace

Ya kwatanta yadda fadar shugaban kasa ta ke alawadai da matsalolin tsaro a matsayin abin ban takaici, inda ya ce alawadan ba ya dakatar da kashe-kashen.

Tsohon Jagoran sojin kamar yadda Daily Trust ta nuna, ya ce rashin tsaron yana ci gaba ne saboda Buhari ba ya da masu ba shi shawarwari na kwarai, kawai suna morar romon demokradiyya ne.

Kara karanta wannan

Sau uku Ubangiji na kirana, ya ce Atiku ne zai gaji Buhari a 2023, inji Dino Malaye

A dayan bangaren, wani tsohon shugaban rundunar sojin kasa ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda mulkin nan ke tafiyar da matsalolin rashin tsaro.

Ya kara da cewa dasa bama-bamai a dajika ba mafita bane, ya kamata gwamnatin tarayya ta gano tushen matsalar don ta san mafita.

Idan kana son kashe bishiya tun daga tushenta za ka tumbuke ta inji shi

Kamar yadda ya ce:

“Idan kana son kashe bishiya, cire tushenta za ka yi saboda idan ka yanke rassanta ba tare da tumbuke tushe ba, ba ka kashe ta ba. Don haka dasa bama-bamai a dajika ba mafita bane a gani na.”

A nashi bangaren, Kaftin Rufai Garba, tsohon shugaban rundunar soji na Anambra da Sokoto ya ce ya kamata a zauna da sojoji da shugabannin al’umma don tattaunawa.

Ya ce ya yarda da cewa gwamnati ba ta kokarin zama da shugabannin anguwanni don kokarin gano mafita ga matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Korarren Limamin Abuja ya magantu, ya sanar da sabon mukamin da ya samu

Group Captain na rundunar sojin saman Najeriya, John Ojikutu ya ce samo bayanan sirri ne mafita ga matsalar tsaro a kasar nan. Ya ce matsawar ba a yi hakan ba babu yadda za ayi a fita daga matsalar.

Ya kamata shugaban kasa ya dinga amfani da bayanan sirri

Okhidievie mai murabus ma ya ce shugaban kasa ba ya gano bayanan sirri na asali, ana kawo masa tatattun bayanai ne kawai.

Ya kuma ce an mayar da harkar tsaro siyasa, ya kamata a yi gaggawar cire siyasa don kawo karshen wannan matsalar.

Wani tsohon mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda, Ambrose Aisabor ya ce an riga an lalata tsaron kasar nan gaba daya.

Kamar yadda ya ce:

“Kuna fada mana cewa sojoji suna aiki a jihohi 34 kuma babu wani ci gaba? To me ke faruwa?”

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

Kara karanta wannan

'Yan siyasan PDP ne suka sankame albashin sojoji a aljifansu, inji gwamnatin Buhari

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel