'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi

  • Hukumar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da damke wani magidanci mai suna Ahmadu Shu'aibu mai shekaru 40 a duniya
  • 'Yan sandan da ke sintiri ne suka kama shi da bindiga kirar AK-47, harsasai masu rai, shanu 31, tumaki 28 da kare guda 1
  • Wanda ake zargin ya amsa cewa ya siya makaman ne daga wurin wani Ibrahim tun daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya

Bauchi - Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta yi ram da wani magidanci mai shekaru 40 a duniya bayan ta kama shi da bindiga kirar AK-47 da kuma harsasai masu rai.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, 5 ga watan Afirilu.

'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi
'Yan sanda sun cafke magidanci da bindiga, carbin harsashi 20, shanu 31 da tumaki 28 a Bauchi. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC
"A ranar 15 ga watan Maris na 2022 wurin karfe 8 na safe, jami'an hukumar mu da ke sintiri a yankin Nabordo da ke karamar hukumar Toro ta jihar Bauchi sun kama wani mutum mai suna Ahmadu Shuaibu mai shekaru 40 a duniya mazaunin Ruwaji da ke Bakin Ruwaji a karamar hukumar Toro," yace.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Mubarak Bala wanda aka daure saboda batanci ga Annabi

"An bincike shi sosai inda aka gane yana dauke da bindiga kirar AK-47, carbi 20 na harsasai masu tsayin 7.62mm, tumaki 28, shanu 31 da kare 1."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin binciken, wanda ake zargin ya amsa cewa ya siyo makaman ne daga wani mutum mai suna Ibrahim daga jihar Taraba, shafin LIB suka ruwaito.

"Ana cigaba da bincike kuma za a mika wanda ake zargin gaban kotu bayan kammala bincike," kakakin rundunar 'yan sandan ya kara da haka.

'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane

A wani labari na daban, jami’an ‘yan sanda a Kano sun yi nasarar bindige wasu masu garkuwa da mutane a kalla uku tare da ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a hannunsu, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Kakakin rundunar ‘yan sandanjihar, SP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kano a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an kashe masu garkuwar ne a wani artabu da ya barke tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami'an tsaro.

Vanguard ta ruwaito cewa, SP Haruna ya ce an kubutar da wadanda aka sace ba tare da jin rauni ba, kuma tuni aka mika su ga iyalansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel