Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

Sabon hari: Bayan ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22

  • Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a wata hanyar Abuja zuwa Kaduna a jiya Lahadi
  • Wannan lamari ya faru ne jim kadan bayan da IGP na 'yan sanda ya kai ziyara yankin bayan harin 'yan bindiga
  • Ya zuwa yanzu an ce mutane 22 ne aka yi garkuwa dasu, amma wasu sun tsere kana 'yan bindigan sun jefar da wata mata

Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kai samame a wasu gidaje a Anguwar Maji, cikin garin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu mutane 22 bayan sa’o’i 24 da ziyartar babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba.

Jere, wanda ke da iyaka da Tafa-Sabon-Wuse a Jihar Neja, na kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Sabon harin 'yan bindiga a Abuja
Sabon hari: Bayan kai ziyarar IGP Kaduna, 'yan bindiga sun bi gida-gida sun sace mutane 22 | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Anguwar Maji, Shehu Bala, wanda ya tabbatar da sace mutanen a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren Lahadi.

Ya ce ‘yan bindigar wadanda suka zo da yawa dauke da bindigu kirar AK-47, sun mamaye wasu gidaje inda suka yi awon gaba da mutane 22 ciki har da mata biyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, ‘yan bindigar sun shafe sama da awa daya suna gudanar da ayyukansu na barna a yankin.

Ya kara da cewa sun fara harbe-harbe ne kawai don tsoratar da mutane daga bin su bayan aikata barnar da tserewarsu.

Shehu Bala ya ce daya daga cikin mutanen 22 da aka yi garkuwa da su ya tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi yayin da suke tafiya dasu cikin daji.

Wani da aka sace makwabcinsa ya ce ‘yan bindigar sun zo ne da misalin karfe 10 na dare inda suka yi garkuwa da mutane 14, inji rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane

A cewar majiyar, daga baya mutane uku sun tsere sannan 'yan bindigan suka jefar da wata mata da rashin lafiya ya kama.

Ya shaida cewa:

“Sun yi garkuwa da Alhaji Kasuwa da matarsa Aunty Kubacha da yaronsu. Sun kuma yi garkuwa da Malam Sule Maishago tare da iyalansa baki daya."

Ya zuwa yanzu dai ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalinge ba.

Harin Abuja-Kaduna: Har yanzu ba a ji duriyar fasinjojin jirgin kasa 146 ba, NRC

A wani labarin, har yanzu ba a ji duriyar mutum dari da arba'in da shida cikin fasinjoji 362 da ke cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, kwanaki shida bayan harin da 'yan ta'adda suka kai kan jirgin.

Manajan daraktan hukumar kula da layin dogo ta Najeriya, Mista Fidet Okhiria ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka samo a ranar Litinin 4 ga watan Afirilu.

Kara karanta wannan

El-Rufai: Mun san inda 'yan bindiga suke, abu daya ne ya hana mu farmaki maboyarsu

Rahoton Punch ya bayyana cewa, adadin fasinjojin da suka tsira ya karu zuwa 186 tun bayan harin na kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.