Ta'addanci: Na kaɗu da kashe-kashen dake faruwa a kusa da birnin Abuja, Kwankwaso ya yi magana

Ta'addanci: Na kaɗu da kashe-kashen dake faruwa a kusa da birnin Abuja, Kwankwaso ya yi magana

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce abubuwan dake faruwa a kusa da Abuja abun mamaki ne da kaɗuwa
  • Kwankwaso, wanda tsohon ministan tsaro ne a Najeriya, ya ce Obasanjo ya bar Sojoji da karfi da horon da zasu iya kare martabar ƙasa
  • Ya kuma shawarci gwamnati ta yi duk me yuwuwa wajen ganin mutanen da suka yi imani da ita sun zauna lafiya

Abuja - Tsohon ministan tsaro, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kashe-kashen da yan ta'adda ke yi kusa da birnin tarayya, Abuja.

Kwankwaso ya yi wannan furucin ne yayin da ya bayyana a kafar watsa labarai Channels tv a cikin shirin 'Siyasa a yau'.

A cewarsa, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bar dakarun sojoji da ƙarfi, horo, kuma a shirye suke su kare duk wani nau'in ta'addanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Sojoji sun samu gagarumar nasara kan Boko Haram/ISWAP a wani gumurzu

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ta'addanci: Na kaɗu da kashe-kashen dake faruwa a kusa da birnin Abuja, Kwankwaso ya yi magana Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto Kwankwaso ya ce:

"Abun ba daɗi baki ɗaya yan Najeriya mun tsinci kan mu a wannan halin. Lamarin tsaro ba Najeriya kaɗai ba, a duniya baki ɗaya abu ne mai muhimmanci, hakan yasa kundin mulkin kasa ya ba da fifiko a tsaro, rayuwa da dukiyoyi."
"Ina Alfahari da cewa na rike ministan tsaro lokacin wa'adin mulkin Obasanjo na biyu kuma Ofishina na samu ikon aiki tare da Sojoji. Na yi amanna mun bar Sojojin da zasu iya kare ta'addanci a Najeriya."
"Na jagorance su zuwa ƙasashen duniya, musamman anan Afirka da sauran sassan duniya kuma sun samu nasara sun dawo gida lami lafiya. Abin da ke faruwa yanzu a gani na, canjin shugabanci ne, suna iya kokarin su."

Mun kaɗu da mamakin abubuwan dake faruwa - Kwankwaso

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

Tsohon gwamnan Kano ya ƙara da cewa abin da kowa ke gani a yanzun, abu ne mai matuƙar sa kaɗuwa da kuma ban mamaki.

"Mu jingine duk wannan, abin da ke faruwa yanzun, a karan kaina da duk wani mai alaƙa da Sojoji da sauran hukumomin tsaro, abun kaɗuwa ne da ban mamaki cewa wasu abubuwa na faruwa kusa da Abuja."
"Yana faruwa daga nan zuwa Kaduna da kuma wasu sassan ƙasar nan. Ina da yaƙinin lokaci ya yi da zamu shawarci gwamnati ta yi duk mai yuwuwa wajen inganta rayuwar mutanenta."

A wani labarin kuma Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

Sojojin Najeriya sun sheƙe yan ta'adda aƙalla 34 a wani ƙauye dake iyaka tsakanin jihar Kaduna da Neja.

Majiyar Sojoji ta bayyana cewa sun samu bayanan sirri na ganin yan ta'adda 70 a kan babura 40 wasu kuma aƙasa sun nufi hanyar Akilibu- Sarkin Pawa.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Asali: Legit.ng

Online view pixel