Makarantun firamare: Gwamnan Katsina ya ba da umarnin a fara karantarwa da harshen Hausa

Makarantun firamare: Gwamnan Katsina ya ba da umarnin a fara karantarwa da harshen Hausa

  • Gwamna Bello Masari ya bukaci cibiyoyin kula da tsara manhajojin karatu a matakin farko da su rungumi amfani da harshen gida wajen koyar da yara a matakin farko na karatunsu
  • Ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da littattafai guda uku na adabin Hausa wanda Malam Mande Muhammad ya rubuta
  • Masari ya ce gwamnati za ta ci gaba da bunkasa adabin Hausa domin kiyaye al’adu da kayayyakin tarihi na jihar

Katsina - Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya umurci malamai a cibiyoyi daban-daban na ilimi a jihar da su fara koyar da yara da harshen gida.

Masari ya bayar da wannan umarni ne a lokacin kaddamar da wasu litattafai uku da suka shafi wakoki da adabi a kasar Hausa da kuma fassarar kamus na Turanci zuwa harshen Hausa wanda Mande Muhammad ya rubuta.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Gwamnan Katsina ya magantu kan tsarin ilimin firamare
Ku koyar da dalibai da yaren Hausa: Gwamnan Katsina ya kawo sabon tsarin karantarwa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An yi bikin kaddamawar ne a ranar Alhamis 31 ga watan Maris a Katsina, The Guardian.

Gwamnan wanda kwamishinan ilimi, Farfesa Badamasi Charanchi ya wakilta, ya bayyana cewa irin wannan tsarin na koyarwa zai taimaka wa yara wajen inganta ilminsu.

Ya bayyana cewa an tsara manufofin kasa kan ilimi ne domin koyar da yara daga tushe cikin harsunan gida.

Masari ya yabawa marubucin kan rubuta litattafai cikin harshen Hausa, inda ya bayyana yunkurin a matsayin wani shiri abin yabawa kuma mai kawo ci gaba a cikin al'umma.

Mai kishin jama'ar karkara ya gina makaranta a kungurmin kauyen da basu san Boko ba

Yayin da mutane da dama ke koka yadda gwamnati ta gaza wajen tabbatar da ingantaccen ilimi ga alummar kasar nan, wani mutum a jihar Gombe ya zo da sabon tsarin habaka ilimi.

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

Ambasada Habu Ibrahim Gwani, wani mazaunin jihar Gombe ne da ya gina wata makarantar firamare a wani kungurmin kauye mai suna Agangaro da ba kowace irin mota ce ke iya shiga ba.

Kauyen Agangaro, wanda hedkwata ne ga wasu rugagen Fulani a yankin Gwani yamma ta karamar hukumar Yamaltu a jihar Gombe, a zagaye yake da mutane da dama, wadanda ke rayuwa ba tare da sanin yadda ake karatu da rubutu ba.

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar Gombe, ya yi tattaki wajen taron budewa da mika makarantar ga gwamnatin jiha har wurin da aka yi ginin, inda ya tattaro bayanai tare da tattaunawa da mutumin da ya yi wannan aikin.

Jinkiri alheri: Duk da shafe shekaru biyu a aji daya a jami'arsu, yanzu ta gama da '1st Class'

A wani labarin, wata ‘yar Najeriya mai suna Ogunsanya Oluwafunke Esther, ta bayyana a yanar gizo domin nuna farin cikinta kan kammala digirin farko da sakamako mafi kyau (1st class).

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

A wani rubutu da ta yi a Twitter, budurwar ta bayyana cewa ta bata shekaru biyu (2016 da 2017) a ajin farko na jami'a. Hakan ya sake faruwa da ita a shekararta ta karshe yayin da ta sake shafe shekaru biyu (2020 da 2021) a ajin na karshe.

Oluwafunke ta bayyana cewa jinkiri ba komai bane wani lokacin face alheri, domin a karshe ta cimma burinta. Budurwar dai ta godewa Allah bisa wannan nasara da ta samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.