Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

  • Bayan sakaya tsohon shugaban rundunar bincike ta sirri, Abba Kyari, a gidan yarin Kuje, ya ki amincewa da abincin gidan yari
  • Dakataccen mataimakin kwamishinan ya bukaci abincin da matarsa ta shirya masa ko kuma wanda ‘yan uwansa suka kai masa
  • Dama Kyari yana fuskantar tuhuma ne akan safarar miyagun kwayoyi, kuma babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki bayar da belinsa

FCT, Abuja - Tsohon shugaban rundunar binciken sirri, DCP Abba Kyari ya ki amsar abincin da aka ba shi a gidan gyaran halin da aka sakaya shi a ranar Litinin, The Punch ta ruwaito.

Dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci abincin da matarsa ta kai masa ko kuma wanda wani cikin ‘yan uwansa ya kai masa.

Kara karanta wannan

Yadda Jami’an tsaro suka yi burus duk da an samu rahoton za a kai wa jirgin kasa hari

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa
Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dama Kyari ya gurfana gaban kotu ne bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi, kuma babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja ta ki bayar da belinsa.

Hukumar yaki da fasakwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA ta zargi Kyari da wasu jami’an ‘yan sanda 4 da rufa-rufa da kuma harkar hodar ibilis mai nauyin 17.55kg.

Akwai mazauna gidan yarin da ke ta murna da zuwan Kyari

Alkalin, Justice Emeka Nwike, ya umarci hukumar ta mayar da wanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali, jim kadan bayan kin amincewa da bayar da belinsa.

Kotun ta tsaya akan cewa NDLEA ta gabatar da duk wasu abubuwan da suka dace a hana belin Kyari da sauran wadanda ake zargi, Sunday Ubia, Simon Agirgba da John Nuhu, wadanda duk tsofaffin mambobin IRT ne.

A ranar Laraba, bincike ya nuna cewa Kyari da sauran wadanda ake zarginsu sun rabe kawunansu tun isarsu a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta saya wa NDLEA na'urar gane mutum idan ya sharara karya

Wakilin The Punch ya tattaro bayanai akan cewa zuwansu ya faranta wa ‘yan gidan yarin rai, wadanda DCP din ya yi bincike akan laifukan da suka yi karkashin IRT.

Wani jami’i ya ce:

“Mun yi zargin ba zai ci abincin da ake bayarwa a nan ba. Don haka bamu yi mamaki ba da muka ji ya bukaci abinci daga wurin matarsa ko ‘yan uwansa.
“Zuwansa ya kawo farin ciki da murna a cikin gidan yarin. Yawancin mazauna gidan sun taba shiga hannunsa kuma suna ta maganganu akan cewa ga dan sanda a gidan gyaran halin Kuje, mutumin da ya yi bincike akan wasunsu.”

An halasta dan uwan mutum ya kai masa abinci ko kuma wani amintaccensa

Kakakin hukumar gidan yarin, Francis Enobore, ya ce mazauna gidan yarin suna da damar cin abincin da ‘yan uwansu suka kai musu. Kuma zasu iya samar wa da kansu abinci.

A cewarsa:

“Dokar mu ta bayar da dama ga mazauna gidan yari su ciyar da kansu amma sai sun tura wasika ga hukumar gidan. Jami’in da ke kan aiki ne yake da damar amincewa ko kuma ya ki. Daga nan sai a san wanda zai dinga kai abincin.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

“In har wanda zai kai abincin bai kai ba, ba za a zuba wa mutum abincin gidan ba. Kuma wajibi ne wanda ya kai abincin ya dandana kafin a mika shi ga mutum.”

Enobore ya ce ba sa amincewa da giya ko taba, kuma yanzu haka akwai jami’an gidan yarin guda 12 da suke fuskantar hukunci saboda shiga da haramtattun abubuwa gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel