Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

  • A ranar Litinin, 28 ga watan Maris, ne aka wayi gari da wani mummunan al’amari a Najeriya bayan wasu yan bindiga sun farmaki wani jirgin kasa da ke hanyar zuwa Kaduna
  • A yayin harin wasu fasinjoji sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata
  • A nan Legit ta zakulo dan takaitaccen bayanai na wasu mutane hudu da suka kwanta dama ta sanadiyar harin

Ranar Litinin, 28 ga watan Maris, ta kasance ranar bakin ciki ga yan Najeriya bayan wasu yan bindiga sun farmaki wani jirgin kasa da ke hanyar zuwa Kaduna sannan suka kashe wasu fasinjoji.

Yan ta’addan sun tayar da bam a kan hanyar layin dogo daga Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya sa jirgin mai dauke da daruruwan fasinjoji kauce hanya.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Sunaye da lambar wayoyin mutum 398 da suka sayi tikirin jirgin Abuja zuwa Abuja

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna Hoto: @AshakaSaleh, @DuruchibuzorE, @daily_trust, @nmanigeria
Asali: Twitter

Sai suka fara harbi kan mai uwa da wabi bayan sun tilastawa jirgin kasan tsayawa, inda suka kashe akalla fasinjoji takwas da kuma raunata wasu 26. Ba a ga wasu fasinjoji da dam aba yayin da bayanai suka nuna cewa sama da mutum 300 ne a cikin jirgin da aka kaiwa hari.

Ga dan takaitaccen bayanan wasu mutane hudu da aka gano cikin wadanda suka mutu a harin:

1. Dr Chinelo Nwando

A cewar sashin BBC News Pidgin, Dr Chinelo Nwando na aiki da asibitin St Gerald Hospital a Kaduna.

Aisha Mustapha, sakatariyar kungiyar likitocin Najeriya (NMA), reshen jihar Kaduna, wacce ta tabbatar da mutuwar Chinelo ta ce ya kamata ace ta tafi kasar Canada a ranar Juma’a kafin mummunan harin da ya yi sanadiyar mutuwarta.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

Kungiyar NMA ta bayyana marigayiyar likitan a matsayin jajirtacciya, cewa za su yi kewanta sosai.

2. Barista Musa Lawal Ozigi

Barista Musa Lawal Ozigi ya kasance babban sakataren kungiyar yan kasuwa ta TUC a Najeriya.

Shugaban kungiyar TUC, Kwamrad Quadri Olaleye ne ya tabbatar da mutuwar nasa.

3. Kwamrad Akinsola Akinwunmi

An kashe Shugaban TUC reshen jihar Kwara, Kwamrad Akinsola Akinwunmi, a harin jirgin kasan.

Kwamrad Olaleye wanda ya kuma tabbatar da mutuwar Akinwunmi ya ce su biyun suna a hanyarsu ta zuwa Kaduna domin wani taro wanda ya kamata ayi a ranar Talata, 29 ga watan Maris.

4. Abdu Isa Kofar Mata

Kafin harin jirgin kasan wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa, Abdu Isa Kofar Mata, ya kasance daraktan hukumar kula da ilimin fasaha.

Kaninsa Mukhtar ya ce yam utu ne daga harbin bindiga, inda ya kara cewa mutuwar Isa ya saka ahlin cikin halin dimuwa.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

An bayyana marigayin a matsayin mutumin da ke taimakon mutane masu bukatar taimako a kodayaushe.

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

A wani labari, ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya bukaci yan Najeriya da su kawo gudunmawar kudi domin kula da wadanda harin jirgin kasa na ranar Litinin ya ritsa da su.

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da yan bindiga suka far ma jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Amaechi, wanda ya ziyarci wajen harin a ranar Talata, ya ce ba don an toshe sayan manyan kamarori da na’urori na layin dogo da kudinsu ya kai naira biliyan 3 ba, da an dakile harin, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng