Harin hanyar Abuja-Kaduna: An harbi Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara a harin jirgin kasa

Harin hanyar Abuja-Kaduna: An harbi Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara a harin jirgin kasa

  • Tsohon mataimakin gwamnan Zamfara, Ibrahim Wakkala, na a cikin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka kaiwa hari a ranar Litinin
  • Wakkala ya samu rauni ta sanadiyar harbin bindiga bayan tawagar tsaro sun ceto shi daga hannun yan bindigar da suka yi garkuwa da shi a yayin harin
  • Yana a hanyarsa ta dawowa ne daga babban taron gangamin APC da aka yi a karshen mako

Kaduna - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala, ya ji rauni daga harbin bindiga a harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Yan bindiga sun far ma jirgin kasan da ke dauke da daruruwan fasinjoji a tsakanin Katari da Rijana a jihar Kaduna.

Wani hadimin tsohon mataimakin gwamnan ya fada ma talbijin din Channel cewa an harbi Mista Wakkala ne wanda ke dawowa daga babban taron APC da aka yi a ranar Asabar a yayin musayar wuta tsakanin yan ta’addan da sojoji.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

An harbi tsohon mataimakin gwamnan Zamfara a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna
An harbi tsohon mataimakin gwamnan Zamfara a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna Hoto: News Digest Nigeria
Asali: UGC

Ya kuma ce an kwashe shi zuwa wani asibitin sojoji da ke Kaduna domin jinya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara, Yusuf Idris ya kuma tabbatar da lamarin ga gidan talbijin din.

Idris ya ce da farko yan bindiga sun sace tsohon mataimakin gwamnan a yayin harin amma sai tawagar hadin gwiwa ta DSS da sojoji suka yi nasarar ceto shi.

“Da farko sun sace shi amma sai DSS da sojoji suka ceto shi, a cikin haka ne ya ji rauni ta sanadiyar harbin bindiga a kafarsa.
“Ya daidaita sosai a yanzu, yana samun kulawar likitoci a asibitin jihar Kaduna.”

Daily Trust takuma nakalto Idris na kara cewa:

“Yana samun sauki sosai. Yana amsa kiraye-kirayen waya a gadonsa na asibiti. Na yi magana da shi kuma wasu mutane da dama ma sun yi. Babu wani abun tashin hankali.”

Kara karanta wannan

Harin filin jirgin saman Kaduna: 'Yan bindiga tserewa suka yi da ganin jami'anmu, gidan soja

Harin jirgin kasa: An gano gawarwakin mutane da yawa a wurin da 'yan bindiga suka kai hari, Gwamnatin Kaduna

A gefe guda, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da cewar an rasa rayuka a harin ta’addanci da aka kai kan jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Talata dauke da sa hannun kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, Daily Trust ta rahoto.

Sai dai kuma, Aruwan bai bayyana adadin mutanen da suka mutu ba amma ya ce an kwashi wadanda suka rasa rayukan nasu da wadanda suka jikkata zuwa asibiti. Ba a kuma ambaci sunan asibitin da aka kaisu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel